Kullu Nafsin Za'ikatul Maut: Amarya da Ango sun mutu a cikin daren amarcinsu

Kullu Nafsin Za'ikatul Maut: Amarya da Ango sun mutu a cikin daren amarcinsu

- Wata sanarwa da muka samu ta nuna yadda amarya Sumayya da mijinta suka mutu a daren jiya a garin Minna babban birnin jihar Neja

- An bayyana cewa Sumayya da mijin nata sun kwanta a daren jiya Talata lafiyarsu lau, sai dai kawai an tashi duka an iske gawarwakinsu

- Yanzu haka dai an gabatar da ga mamatan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada

Wani rahoto da muka samu ya nuna yadda Sumayya da mijinta suka mutu a daren jiya a garin Minna babban birnin jihar Neja.

Rahotanni sun nuna cewa amarya da angon sun kwanta a daren ranar Talata lafiya lau, sai dai kuma an wayi gari aka gansu sun rasu gaba daya.

Sumayya da mijinta dai ba su jima da angwancewa ba, inda suke tsakar shan soyayya irinta ango da amarya kafin rai yayi halinsa.

KU KARANTA: Tirkashi: Basa bada sadakar ko sisi, shine yasa na saci mota domin na biya bashin da ake bina - Wani Limami ya koka

Wannan sanarwa ta rasuwar ta fito daga bakin Abdulsamad Kabiru Musa, wanda yake Yayane a wajen marigayiya Sumayya.

Tuni dai Abdulsamad ya bayyana cewa an yiwa amarya da angon jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Muna addu'ar Allah ya jikansu ya gafarta musu, mu kuma idan tamu ta zo Allah yasa mu cika da kyau da imani, Ameen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel