Sunaye da mukami: An zabi sabbin shugabanni a Kannywood

Sunaye da mukami: An zabi sabbin shugabanni a Kannywood

Kungiyar Masu Shirya Fina-finai na Arewa ta Najeriya 'The Arewa Film Makers Association of Nigeria', AFMAN ta kammala zaben sabbin shugabanin ta.

An gudanar da zaben cikin zaman lafiya da lumana a ranar Asabar 17 ga watan Augusta a garin Kano kuma an mika wa wadanda su kayi nasarar takardun shaida wato satifiket.

Anyi takarar kujeru daban-daban kuma daga karshe an samu wadanda suka lashe zaben.

Tsaffin jaruman Kannywood wanda kuma suna cikin kwamitin amintattun na kungiyan ne suka gudanar da zaben a Kano.

A yayin da ya ke sanar da sakamakon zaben, Shugaban kwamitin zaben, Salisu Mohammed ya ce anyi adalci yayin gudanar da zaben.

"Munyi zabe cikin adalci da aminci kuma an samu wadanda suka yi nasara. Dukkan wadanda su kayi nasara a zaben da su rike mukammai a kungiyar daga yanzun zuwa shekarar 2021 kafin a sake zaben sabbin shugabanni." inji Mohammed.

DUBA WANNAN: Tsaffin gwamnonin da suka shiga taska mai wuya bayan barin mulki a 2019

Ga jerin sunayen wadanda suka yi nasara da mukamansu:

1. Jamilu Yakasai - Shugaban AFMAN

2. Lawal Ahmed - Mataimakin Shugaba

3. Abdullahi Habibu - Audita

4. Aminu Dambazau - Mataimakin Sakatare

5. Rabiu The King - Sakataren Tsare-tsare

6. Abubakar Gboy - PRO

7. Halima Ateteh - Mai kula da walwala

8. Hannatu Bashir - Sakataren Kudi

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel