Ke duniya: An kama wani yaro dan shekara 15 da ya yiwa iyayensa karyar an sace shi don su bashi rabin miliyan kudin fansa

Ke duniya: An kama wani yaro dan shekara 15 da ya yiwa iyayensa karyar an sace shi don su bashi rabin miliyan kudin fansa

- Jami'an 'yan sanda sun kama wani karamin yaro mai shekara sha biyar a duniya, wanda ya zabgawa iyayensa karya haka siddan

- Yaron ya yiwa iyayensa karyar cewa an sace shi ne saboda yana so su bashi wasu kudade da zai yi wani uzurinsa dasu

- Yaron ya bayyana cewa da gangan ya shirya wannan karya domin iyayensa su bashi dubu dari biyar da zai sayi kayan sawa na zamani

Rundunar hukumar 'yan sandan jihar Filato ta cafke wani dan karamin yaro mai shekaru goma sha biyar da ya shirya karyar cewa anyi garkuwa dashi haka siddan saboda yana so iyayensa su bada kudin fansa naira dubu dari biyar.

Da yake magana da manema labarai a garin Jos babban birnin jihar ta Filato, yaron ya bayyana cewa yayi hakan ne saboda yana so ya samu kudin da zai siyi kayan sakawa na zamani akan wani biki da abokansa suka hada saboda shima ya haska a wajen.

KU KARANTA: Bayan shafe shekaru ba a ji duriyarta ba, jaruma Kubura Dako ta bayyana cikin wani yanayi a wani hoto

"Da gangan na shirya wannan karyar, saboda kudin da nake nema don sayen kayan sawa da zani biki da wasu abokanmu suka hada."

Kwamishinan 'yan sandan jihar Isaac Akinmoyede ya sanar da cewa rundunar tasu ta kama wasu mutane guda hudu da suke da hannu a wannan karya da yaron ya shirya ta damfarar iyayensa.

"Mahaifin yaron ne yazo ofishinmu da kansa ya bayyana cewa tun da safe da yaron ya fita wajen koyon aiki bai dawo ba sai can daga baya aka kira shi a waya ake cewa ya bayar da kudin fansa naira dubu dari biyar."

Kwamishinan ya bayyana cewa wannan daliline yasa suka bazama neman inda wadannan mutane suke, inda a karshe suka kama yaron da abokanan aikinsa guda hudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel