Hawaye sun kwaranya yayinda Buhari ya nuna alhini kan mutuwar daliban ATBU bayan rufatawar gada

Hawaye sun kwaranya yayinda Buhari ya nuna alhini kan mutuwar daliban ATBU bayan rufatawar gada

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ta’aziyya ga iyalan daliban jami’ar Abubakar Tafawa Balewa University (ABTU), jihar Bauchi, wadanda suka mutu a daren ranar Litinin, ga watan Agusta biyo bayan rushewar wata gada a sansanin jami’ar da ke Gubi bayan zubar ruwan sama kamar da bakin kwarya.

A wani jawabi daga kakakin Shugaban kasar, Mallam Garba Shehu, wanda shima yayi wa hukumar makarantar, dalibai da ma’aikatan jami’ar jaje, ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki wanda ba a shirya ma faruwarsa ba, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa Shugaban kasar ya kuma bukaci hukumomin jami’ar da su kula da kariyar dalibai wadanda ke karkashin kulawarsu.

Ya nuna bakin cikin cewa, “wadannan shugabanni na gaba da iyalansu da za su amfana da su sun hadu da karshensu a wannan hali.”

KU KARANTA KUMA: Gwamnati bata da ikon kama Sowore – Balarabe Musa

Buhari yayi wa mamatan addu’an samunjin kai daga Ubangi, sannan kuma yayi addu’an Allah ya ba iyalansu juriyar wannan rashi. Sugaban kasar ya kuma yi wa daliban da suka jikkata addu’an samun lafiya.

A baya Legt.ng ta rahoto cewa Hukumar makarantar jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi ta ruffe makarantar na tsawo makonni biyu biyo bayan annobar ambaliyar ruwa da yayi sanadiyar mutuwar dalibanta.

Shugaban jami'ar, Abdulazeez Ahmed ya sanar da Channels TV cewa dalibai hudu ne suka mutu a annobar yayinda wasu takwas sun jikkata.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel