Boko Haram: Ba mu da wata makabartar binne sojoji ta sirri - Rundunar soji

Boko Haram: Ba mu da wata makabartar binne sojoji ta sirri - Rundunar soji

A ranar Laraba ne wata jaridar kasar Amurka mai suna 'Wall Street Journal' ta wallafa wani rahoto da ke cewa rundunar sojojin Najeriya ta binne a kalla sojojinta 1000 a sirrance bayan mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe su a jihar Borno.

Kazalika, kafafen yada labarai da dama a cikin gida Najeriya sun yada rahoton jaridar bayan fitowarsa a ranar Laraba, 31 ga watan Yuli.

Sai dai, a ranar Alhamis, 1 ga watan Agusta, rundunar sojin Najeriya ta yi Alla-wadai da rahoton tare da yin watsi da shi.

Rundunar sojin ta bayyana cewa irin wanna rahoto na fitowa ne daga mutanen da basu masaniyar komai a kan atisayen rundunar soji da kuma yadda ta ke gudanar da al'amuranta, a saboda haka ta ce ya zama dole ta fitar da jawabi domin sanar da jama'a al'adar rundunar ta girmama jarumanta da aka kashe a filin daga.

"Bisa tsarin rundunar sojin Najeriya, muna girmama dukkan dakarun soji da suka mutu a filin yaki kuma muna bin dukkan matakan binne su bisa girmama wa, kamar yadda ake yi a duk fadin duniya.

DUBA WANNAN: Ina da alkaluman kuri'un mutanen ka, amsar Buhari ga wani Basaraken kudu da ya nemi alfarma a wurinsa

"Ana yi musu fareti, rera wakokin bankwana a gefen kaburburansu da kuma yi musu addu'ar samun jin kai bisa tsarin addinin Kiristanci da Musulunci da yi musu jinjina ta hanyar harba bindiga da sauran karrama wa da ake yi wa gawarr sojoji," a cewar rundunar soji cikin jawabin da ta fitar a shafinta na Tuwita.

Kazalika, rundunar sojojin ta bayyana cewa makabartar da aka ambata a rahoton, 'Maimalari military Cantontment', mallakar rundunar soji ce, kuma an gina ta ne domin binne jaruman rundunar soji na gida da na waje da suka mutu a filin yaki.

Rundunar sojojin ta yi kira ga dakarunta da sauran jama'a da su yi watsi da rahoton cewa tana binne sojojin da suka mutu a sirrance, ba tare da girmama su ba. Ta ce marubucin rahoton da wadanda suka wallafa shi sun yi hakan ne ba tare da suna da ilimi ko masaniya a kan ka'idoji da tsarin aikin soja ba, sun yi hakan ne kawai domin kawo rudani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel