Mun yi ram da wasu ‘Yan bindiga 10 a Benuwai da Nasarawa - Sojojin OPWS

Mun yi ram da wasu ‘Yan bindiga 10 a Benuwai da Nasarawa - Sojojin OPWS

Dakarun Sojojin Najeriya na Operation Whirl Stroke, sun damke mutane da-dama daga yankin Benuwai da Nasarawa da a ke zargi da laifin satar dabbobi da garkuwa da mutane a yankin.

Sojojin na Operation Whirl Stroke sun kama mutum 10 da ke addabar wadannan yanki kamar yadda shugaban Dakarun watau Manjo Janar Adeyemi Yekini ya bayyanawa Menama labarai.

Janar Adeyemi Yekini ya yi wannan bayani ne a Garin Makurdi a jihar Benuwai Ranar Asabar, 27 ga Watan Yulin 2019, lokacin da ya gabatar da wadanda a ka kama da laifin a gaban ‘yan jarida.

Yekini ya ce sun kama mutum 5 daga cikin wadannan 'yan bindiga ne a cikin karamar hukumar Toto da Awe Nasarawa, yayin da sauran wadanda a ka kama su ka fito daga a jihar Benuwai.

KU KARANTA: Buhari ya san inda matsalar kasar nan ta ke - Amaechi

Babban jami’in sojan kasar ya kuma kara da cewa sun yi nasarar karbe makamai da su ka hada da bindiga kirar AK-47 a hannun wani ‘dan bindiga wanda a ka harbe wajen artabun da a ka yi.

An yi wannan barin wuta ne a Garin Zaki-Biam kamar yadda shugaban Dakarun na Operation Whirl Stroke ya fadawa ‘yan jarida. Daily Trust ta rahoto wannan a Ranar 28 ga Watan Yuli.

Mutum 3 da a ka cafke a wajen wannan hari yaran gawurtaccen Mai laifin nan ne watau Terwase Akwaza wanda a ka fi sani da Gana. An yi ram da gudan masu laifin ne a Garin Tomata a Benuwai.

Daga cikin makaman da a ka samu a hannun wadannan Miyagu akwai bindigogin AK-47, SLR, da harsashi da kuma wayoyin salula 3 da wata mota kirar Toyota Corolla ta zamani da sauran su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel