Harin kwanton bauna: 'Yan Boko Haram sun kashe sojoji 5, sun raunata da yawa

Harin kwanton bauna: 'Yan Boko Haram sun kashe sojoji 5, sun raunata da yawa

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai wa dakarun soji harin kwanton bauna tare da kashe a Kalla biyar da raunta wasa da dama, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito a ranar Lahadi.

Majiyar jaridar ta shaida mata cewa adadin sojojin da suka mutu zai iya karuwa saboda har yanzu ba a ga wasu sojojin ba bayan harin da mayakan suka kai musu ranar Alhamis a Damboa, jihar Borno.

A cewar majiyar, dakarun sojojin sun je yankin ne domin cigaba da sharar sansanin 'yan Boko Haram, amma sai aka kai musu harin kwanton bauna a hanyarsu.

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallinsu.

DUBA WANNAN: Rashin lafiya: An yanke wa fitaccen jarumin fina-finan Hausa kafa daya (Hotuna)

Kwamandan rundunonin dakarun soji da ke jihar Borno, bigediya janar Bulama Biu, ya tabbatar da gwabza wa tsakanin sojoji da 'yan ta'ddar amma ya ce "rundunar soji ba ta rasa mutum ko daya ba."

Sai dai wata majiya daga cikin rundunar soji da mayakan 'sa kai' (CJTF) ta ce an samu gawar sojoji biyar tare da bayyana cewa wasu sojoji 14 da farar hula biyu sun samu raunuka.

Majiyar ta kara da cewa wasu da dama daga cikin dakarun soji sun bace, har yanzu ba a san inda suke ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel