Oyeyemi ya bada shawara a hana masu babur daukar fasinjoji a kan hanya
Shugaban hukumar da ke kula da harkar titi, Dr. Boboye Oyeyemi ya bayyana cewa ya na so a hana yin acaba a Najeriya, sannan kuma a rika hukunta masu saba dokar titi a fadin kasar.
Boboye Oyeyemi ya na ganin cewa idan har a ka fara kama wadanda ke karya ka’idojin tuki a Najeriya a na hukunta su, za su zama darasi ga masu irin wannan danyen aiki a kan tituna.
Dr. Oyeyemi ya bayyana wannan ne a lokacin da ya gabatar da wata lacca a makarantar tuki da ke cikin jami’ar nan ta jihar Legas (LASU) da ke Garin Ojo a Ranar Laraba, 3 ga Watan Yuni, 2019.
Kamar yadda mu ka ji, shugaban hukumar na FRSC ya yi tir da yadda masu babura ke tukin gangancim su na wasa da dokoki. Oyeyemi ya ce ba a bar Direbobin manyan motoci a gangancin ba.
Corps Marshal Oyeyemi ya nuna cewa rashin tsarin tukin kasar ne ya jawo a ke yin Acaba inda ya nemi a haramta yin kabu-kabu a kan titunan kasar nan, a lokacin da ya ke gabatar da laccar ta sa.
KU KARANTA: Wani bututun mai ya tarwatse ya aika mutane lahira
Babu wadanda ke tukin rashin hankali a kan titi irin ‘Yan acaba inji Boboye Oyeymi. Shugaban hukumar da ke kula da hanyoyin ya ce bai kamata masu yin Okada su na aiki a kan hanyoyi ba.
Ya ce: “Ya kamata duka jihohi 36 na Najeriya su samar da manyan motoci, hade da jiragen kasa domin a rika zirga-zirga…”
“Yawan hadarin titi ya na jawo mutuwar jama’a da dama a kananan kasashe masu tasowa. 90% na Matafiya a Najeriya, su na amfani ne da titi. Inji Shugaban na FRSC.
Sakataren din-din-din na ma’aikatar sufuri na Legas, Dr. Taiwo Salam da kuma mataimakin gwamna Femi Hamza a madadin gwamnan jihar da shugaban Jami’ar LASU sun yi magana a taron.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng