Aiki ga mai kare ka: Rundunar sojin sama ta kashe 'yan bindiga guda 20 a dajin Zamfara

Aiki ga mai kare ka: Rundunar sojin sama ta kashe 'yan bindiga guda 20 a dajin Zamfara

- Rundunar sojin sama a aikin Operation Hadarin Daji sun halaka yan bindiga 20 a jihar Zamfara

- Sun kai harin ne da jirgin yaki bayan sun samu bayanin taruwan yan bindigan yayinda suke wata ganawa a kusa da Munhaye na jihar

- Rundunar sojin sama na aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin cimma manufarsu na kakkabe yan bindiga daga yankin arewa maso yammacin kasar

Jirgin yakin Operation Hadarin Daji ta kashe akalla yan bindiga 20 a wani wuri kusa da Munhaye a jihar Zamfara a wani harin sama da suka gudanar a jiya Talata, 2 ga watan Yuli.

An gudanar da aikin ne bisa ga rahoton kwararru da suka samu da ke nuna cewa akwai yan bindiga da dama da suka taru a wajen domin yin wata ganawa.

Ga dukkan alamu suna tattauana batun yadda za su kaddamar da hari ne akan bayin Allah da ke zaunea garuruwan da ke kewaye da wurin lokacin da sojin suka far masu.

Anyi amfani da jirgin yakin sojin saman Najeriya ne wajen kaddamar da hari a ajen, wanda ke a kilomita 15 daga iyakar jihar Katsina.

KU KARANTA KUMA: Rugar Makiyaya: Gwamnonin kudu maso gabas sun hau tudun na ki

A lokacin da jirgin ya isa wajen sun gaano cewa yan bindigaa sama da 30 sun yi kokarin tserewa yayinda suke ta kokarin bude wuta ga jirgin da ke shirin kaddamar da harn. Sai jirgin yakin ya bude ma yan bindigan wuta, inda aka kashe mutane 20 daga cikinsu.

Rundunar sojin sama na aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin cimma manufarsu na kakkabe yan bindiga daga yankin arewa maso yammacin kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng