Dubu ta cika: An kama wani soja da yake sayarwa da 'yan ta'adda makamai a jihar Kaduna

Dubu ta cika: An kama wani soja da yake sayarwa da 'yan ta'adda makamai a jihar Kaduna

- An cafke wani soja a jihar Kaduna, wanda yake sayarwa da masu garkuwa da mutane makamai

- Sojan ya bayyana cewa mutanen basu bayyana mishi cewa satar mutane suke yi ba

- Ya ce sun bayyana mishi cewa zasu dinga amfani da makaman ne wurin kare kansu daga masu satar shanu

An kama wani soja dan shekara 32 mai suna Corporal Koza Yabiliok, a jihar Kaduna da laifin sayar da alburusai ga wasu wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne da suke addabar mutanen yankin shekara da shekaru.

Da aka bincike shi, Yabiliok ya bayyanawa manema labarai cewa yana sayar da kowanne harsashi guda daya akan kudi naira dari hudu (400). Sojan yana aiki a garin Jaji dake jihar ta Kaduna.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya bayyana abubuwan da gwamnatinsa za ta bawa muhimmanci a wannan zangon

Yabiliok ya bayyana cewa bai taba tunanin cewa abokin kasuwancin nasa dan garkuwa da mutane bane. Ya kara da cewa dan ta'addar kawai ya sanar dashi cewa yana amfani da harsashin domin kare kanshi daga barayin shanu ne. "Haka ne yasa nake siyar mishi da harsashin ban san cewa shi mai garkuwa da mutane ba ne," in ji shi.

A lokacin da yake magana da manema labarai, Kwamishinan 'yan sandan jihar, Ali Aji-Janga, ya ce sun samu nasarar kama mutane 61 da suke da laifuka kala-kala da suka hada da, garkuwa da mutane, fashi da makami, kissan kai da kuma satar shanu. Ya ce sun kuma samu nasarar kwace muggan makamai, harsashi, kwayoyi, da ababen hawa daga wajen 'yan ta'addar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel