Jihohin arewa 7 da aka fi kashe mutane a watan Mayu

Jihohin arewa 7 da aka fi kashe mutane a watan Mayu

A kalla mutane 310 aka kashe a Najeriya a cikin watan Mayu sakamakon aiyukan ta'addanci daban-daban da suka hada da rikicin 'yan bindiga, fashi da makami, da sauran wasu rigingimu da dama.

Katsina, Jihar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na daga cikin jihohin arewa uku da ke sahun gaba a yawan adadin mutanen aka fi kashe wa a Najeriya a watan Mayu, sakamakon aiyukan 'yan ta'adda daban-daban.

Ragowar jihohin arewa biyu su ne; Borno da Zamfara.

Hakan na kunshe ne a cikin wani rahoto na musamman da aka saki a babban birnin tarayya, Abuja, a ranar Alhamis.

Wata kungiya mai bin kwakwkwafi, 'Nigeria Mourns', ce ta hada tare da wallafa rahoton.

A cewar kungiyar, daga cikin mutanen da aka kashe a watn na Mayu akwai dakarun soji guda 22 da jami'an 'yan sanda guda 22.

'Nigeria Mourns' ta bayyana cewar an samu mutuwar mutane 67 a jihar Zamfara sakamakon rikicin 'yan bindiga.

DUBA WANNAN: Tashin hankali: Wata mata ta kashe mijinta, ta yi yunkurin kone gawarsa

An kashe mutane 64 a jihar Borno, mai fama da rikicin Boko Haram.

'Yan bindiga da masu garkuwa da mutane sun kashe mutane 51 a jihar Katisna.

An samu asarar rayuka 29 a jihar Taraba da mutuwar wasu mutanen 26 a jihar Jigawa.

Rahoton ya kara da cewa an kashe mutum 12 a jihar Filato, yayin da a jihar Kogi aka kashe mutum 1.

Matsalar kisan mutane a cikin watan na Mayu ba ta tsaya ga iya kan jihohin arewa ba kadai.

Mutane 18 sun rasa ransu a jihar Ribas, mutane 12 a jihar Edo, 5 a jihar Ebonyi, sai kuma hudu a jihar Ogun da mutum daya a jihar Legas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng