Yan sanda sun kama wasu manyan yan fashi 10 a Gwagwalada

Yan sanda sun kama wasu manyan yan fashi 10 a Gwagwalada

- Hukumar yan sandan Najeriya reshen birin tarayya ta kama wasu yan fashi 10

- Ana dai zargin yan fashin da addabar al’umman garin Gwagwalada da kewayenta

- Daga cikin sunayen yan fashi akwai Mohammad Jamilu, Nasiru Mohammed, Jamilu Jibrin, Atau Abubakar, Nafiu Mohammed, Sadiq Abdullahi, Hashiru Garba, Isiyaku Ahmed da Danjuma Abubakar

Rundunar yan sandan Najeriya reshen birin tarayya ta kama wasu yan fashi 10 masu kaddamar da hare-hare akan al’umman garin Gwagwalada da kewayenta.

A wani jawabin da kakakin birnin tarayyar, DSP Anjuguri Manzah ya gabatar, yace sashin SARS ne suka kama masu laifin bayan an sanar da rundunar.

Yace an kama masu laifin sun wadanda suka kasance mambobin kungiyar yan fashin da ke kai ma al’umma harida mugun makamai cikin wani ginin da ba a kammala ba inda suke amfani dashi a matsayin mabuyansu.

Daga cikin sunayen yan fashi akwai Mohammad Jamilu, Nasiru Mohammed, Jamilu Jibrin, Atau Abubakar, Nafiu Mohammed, Sadiq Abdullahi, Hashiru Garba, Isiyaku Ahmed da Danjuma Abubakar.

Ya kara da cewa masu laifin sun karbi bakin aikata mugun ayyukan da suka hada da fasa gidaje, sace-sacen waya da fashi da makami.

Ya kara da cewa wani mai shekara 54, Salisu Ali ya kasance babban mai siyan kayan sata, inda ya bayyana cewa daga cikin kayan da aka kwato daga hannun masu laifin akwai setin talbijin kirar Plasma, janareto biyu, na’ura mai kwakwalwa uku, adda daya, wuka daya, layoyi, sarkoki, kayan sawa, takalma da sauransu.

KU KARANTA KUMA: An raunata wani Limami a harbin bindiga da aka kaddamar a wajen wani masallaci

Har ila yau Manzah yace jami’an yan sandan ta kama wani mai suna Kamal Gali, wanda ya shahara wajen amfani da makamai don kai ma al’umma hari da kwatan kayayyaki masu amfani.

A cewar shi, an kama mai laifin ne bayan an karbi kara daga daya daga cikin wadanda yayi ma fashi, inda yake cewa jami’an yan sanda sun dauki mataki inda suka gano mafakar dan fashin a jejin Jabi inda aka kama shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel