Akwai masu shirin yi wa Amaechi kazafi don su bata shi - Hadiminsa

Akwai masu shirin yi wa Amaechi kazafi don su bata shi - Hadiminsa

Mun ji labari tsohon Ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa ya fahimci a na shirin shirya wani makirci na yi masa sharri da kazafi da nufin a bata masa suna a Duniya.

Chibuike Rotimi Amaechi ya bayyana wannan ne ta bakin wani Hadiminsa, David Iyofo. Mista Iyofo ya fitar da wannan jawabi a Garin Fatakwal a Ranar Alhamis 27 ga Watan Yuni, 2019.

“Mu na sane cewa a na shirin fito da wasu tarin labarai na bogi da sharri da karyayyaki iri-iri da kuma da takardu na kage da nufin a bata mutunci da darajar da Ubangiji ya yi wa Rotimi Amaechi, kwararre kuma gogaggen ma’aikacin gwamnati.” Inji Hadimin tsohon Ministan.

Jawabin ya ce “Wannan mummunan shiri ne da wasu ke ke kitsawa domin cin zarafin Amaechi a idanun bainar jama’a, ta hanyar amfani da manyan kafafen yada labarai da kuma kafofin sadarwa na zamani.”

KU KARANTA: Magu ya na zargin wani tsohon Hadimin Jonathan da laifin cin kudi

“Daga cikin wannan danyen shiri da a ke yi nufin yi shi ne jefa sunan Amaechi da Iyalinsa cikin sha’anin gudanarwa na hukumar NDDC na Neja-Delta ta hanyar jawo abin da zai bata masa suna.”

David Iyofo ya ce bayan nan kuma akwai wasu kullen-kullen da a ke kitsawa domin a jawowa tsohon Ministan bakin jini a kasar. Sai dai ba a bayyana ainihin wadanda ke da shirin wannan aiki ba.

Hadimin ya yi maza ya sanar da jama’a cewa babu abin da ya hada Amaechi da harkar hukumar NDDC. Iyafo ya ce nufin wannan shi ne a bata duk irin hidimar da tsohon gwamnan ya yi wa kasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel