Harin kwanton bauna: Sojoji sun yi wa 'yan ta'adda mummunan illa a Yobe (Hotuna)

Harin kwanton bauna: Sojoji sun yi wa 'yan ta'adda mummunan illa a Yobe (Hotuna)

Dakarun Soji na 120 Task Force Battalion da ke Goniri a jihar Yobe sunyi nasara kashe 'yan ta'adda masu yawa a wani harin kwanton bauna da suka kai musu misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Laraba.

Sojojin sun kafa tarko ne inda suka jira 'yan ta'addan suka matso kusa sannan suka yi musu luguden wuta a yayin da suka taho a motoccinsu masu dauke da bindigu guda bakwai.

Kakakin Rundunar Sojojin Najeriya, Kwanel Sagir Musa ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Alhamis inda ya ce 'yan ta'addan sun yi niyyar kai hari ne cikin motocci bakwai da babura.

'Yan ta'adda da dama sun mutu nan take yayin da wasu daga cikinsu suka tsere da munannan raunuka sannan sojojin sun kwato makamai da 'yan ta'addan suka bari.

Harin kwanton bauna: Sojoji sun yi wa 'yan ta'adda mummunan illa a Yobe (Hotuna)
Daya daga cikin motoccin 'yan ta'adda da sojojin Najeriya suka lalata a harin da suka kaiwa 'yan ta'addan a Yobe
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Za a gamu da munanan bala'o'i na ambaliyar ruwa a jihohi 30 - NIHSA

Harin kwanton bauna: Sojoji sun yi wa 'yan ta'adda mummunan illa a Yobe (Hotuna)
Bindigu da alburusai da sauran makamai da sojoji suka kwato hannun 'yan ta'adda a Goniri da ke jihar Yobe
Asali: Twitter

Harin kwanton bauna: Sojoji sun yi wa 'yan ta'adda mummunan illa a Yobe (Hotuna)
Alburusai da bindigu da sauran makamai da sojoji suka kwato hannun 'yan ta'adda a Goniri da ke jihar Yobe
Asali: Twitter

Harin kwanton bauna: Sojoji sun yi wa 'yan ta'adda mummunan illa a Yobe (Hotuna)
Motar yaki da sojojin Najeriya suka kwato daga hannun 'yan ta'adda a Goniri da ke jihar Yobe
Asali: Twitter

Kazalika, Shugaban hafsoshin sojin kasa na Najeriya, Laftanat Tukur Buratai ya yabawa sojojin bisa nasarorin da suke samu a cikin 'yan kwana kin nan inda ya bukaci su cigaba da hakan.

Buratai ya kuma shawarci sojojin su cigaba da kasancewa cikin shirin ko ta kwana kuma ya tabbatar musu cewa za su cigaba da samun goyon baya daga gareshi da kuma kasa baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel