Babu wanda ya kama ni a kan fitar da sabuwar waka - Sadiq Zazzabi

Babu wanda ya kama ni a kan fitar da sabuwar waka - Sadiq Zazzabi

Fitaccen mai rera wakokin finaginan Hausa a masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood, Sadiq Zazzabi, ya karyata labaran da ke yawo a wasu kafafen yada labarai da dandalin sada zumunta a kan cewar wata kotu a jihar Kano ta bayar da umarnin a tsare shi.

Mawakin ya bayyana cewar babu wata kotu da ta bayar da umarni a kama shi a kan wakar da ake cewa ya fitar ba bisa ka'ida ba.

A wani labari da jaridar yanar gizo 'al'ummata.com' ta wallafa a ranar Talata, ta ce a tattuanawar ta da Zazzabi ta wayar tarho, ya shaida mata cewa bai san daga ina labarin cewar an kama shi ya samo tushe ba.

Ya kara da cewa shi ma ya wayi gari ne ya ji ana labarin cewa an kama shi saboda wakar da ya rera. Ya bayyana labarin a matsayin kanzon kurege, da bashi da tushe balle makama.

Mawakin ya yi kira ga kafafen watsa labarai da suke tabbatar wa tare da tantance labari kafin su sanar da jama'a sabida guje wa haifar da rudani a tsakanin jama'a.

A cewar Zazzabi, "ba na gaba da kowa a jihar Kano kuma ina zaune da kowa lafiya. Ina kira ga jama'a da su guji yada jita-jita saboda yin hakan ba abu ne mai kyau ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel