Da duminsa: An kama kwararen mayaki na kasa da kasa cikin 'yan Boko Haram a Borno
Rundunar 'Yan sandan Najeriya reshen Jihar Borno ta kama mutane hudu ciki har da wani kasurgumin dan Boko Haram da ya ke cikin wadanda ke kai hare-hare a kasashen ketare.
An kama wadanda ake zargin ne a garin Borno, cibiyar rikicin kungiyar Boko Haram a Najeriya.
Kwamishinan 'Yan sandan Jihar Borno, Mohammed Aliyu ne ya bayar da wannan sanarwan yayin wata taron manema labarai da ya kira a Maiduguri.
DUBA WANNAN: Rikicin jam'iyya: Ana fargabar za a sake dakatar da wani gwamnan APC
"Ali Ibrahim gawurtaccen mayaki ne a kungiyar Boko Haram. An kama shi ne a garin Dikwa. Yana cikin tawagar da suka kai hare-hare a Kamaru, Chadi da Najeriya.
"Mun kuma kama wasu masu hadin gwiwa da mayakan na Boko Haram, wadanda suka saba sayan shanun sata daga hannun barayin shanu," inji kwamishinan 'Yan sandan.
CP Aliyu ya ce a halin yanzu an kama mutane 68 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban tun bayan kaddamar da Operation Puff Adder a jihar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng