An yi bajakolin kayan laifi da masu laifi 32 ciki har da wanda suka sace shugaban UBEC (Hotuna)

An yi bajakolin kayan laifi da masu laifi 32 ciki har da wanda suka sace shugaban UBEC (Hotuna)

- Rundunar 'Yan Sandan Najeriya karkashin Operation Puff Adder sunyi nasarar cafke wadanda ake zargi da garkuwa da mutane 38 ciki har da mutum hudu da ake zargi da hannu cikin satar shugaban UBEC

- Yan sandan sun kwato bindigu 30, bama-bamai guda 77 da shanun sata 160 da kuma buhunnan hatsi 2108

Dakarun 'Yan sanda na Operation Puff Adder sunyi nasarar kama mutane 32 da ke zargi da garkuwa da mutane tsakanin ranar 5 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan cikin su har da mutane hudu da ke zargi da hannu cikin satar shugaban UBEC da diyarsa da kashe direbansa.

A bajakolin da Kakakin 'yan sanda, DCP Frank Mba ya yi a hedkwatan rundunar da ke Abuja ya ce 'yan sandan sun kwato bindigu AK47 11, Kananan bindigan Pistul 12, Bindigun farauta 12, bama-bamai 77, albusai da dama da motoci kisar Volkswagen biyu.

Operation Puff Adder: 'Yan sanda sun kamo wadanda suka sace shugaban UBEC
Masu garkuwa da mutane da jami'an 'Yan sanda suka kama daga jihohin Kaduna, Neja da Katsina
Asali: Facebook

Operation Puff Adder: 'Yan sanda sun kamo wadanda suka sace shugaban UBEC
Motoccin da 'Yan sanda suka kwato daga hannun masu garkuwa da mutane
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Sarki Sanusi ya yi wa 'Yan Majalisar Dokokin Kano nasiha mai ratsa zuciya

Operation Puff Adder: 'Yan sanda sun kamo wadanda suka sace shugaban UBEC
Bindigu, alburusai da khakin sojoji tare da masu garkuwa da mutane da jami'an 'Yan sanda na 'Operation Puff Adder' suka kama
Asali: Facebook

Operation Puff Adder: 'Yan sanda sun kamo wadanda suka sace shugaban UBEC
Kakakin Rundunar 'Yan sanda, DCP Frank Mba yayin baje kollin masu garkuwa da mutane a hedkwatan rundunar da ke Abuja

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164