2019: Masoya sun yi kwana da kwanaki su na rokawa Buhari sa’a

2019: Masoya sun yi kwana da kwanaki su na rokawa Buhari sa’a

Wasu mata na jam’iyyar APC mai mulki sun taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar jagorantar ranar bikin farar hula a Najeriya inda a ka yi bikin murnar zarcewarsa a kan mulki.

Wadannan mata da su ka nemi takarar kujeru da dama a jam’iyyar APC sun hada da yi wa shugaban kasar addu’o’in karin lafiya domin ya jagoranci kasar ba tare da samun matsaloli ba.

Kamar yadda mu ka samu labari, an fara addu’o’in ne a Ranar 26 ga Watan Mayu inda aka kamalla a Ranar Juma’ar nan, 14 ga Watan Yuni, 2019. Adedoyin Eshanumi ta jagoranci taron addu’o’in.

Misis Eshanumi, ta jagoranci sauran Takwarorinta mata da su ka yi takara a APC a zaben 2019, wajen yi wa shugaban kasar addu’a na samun iko, da basira da lafiyar yin mulki babu tasgaro.

Matan sun kuma nemi shugaba Muhammadu Buhari ya rika damawa da su a cikin sha’anin mulki a cikin wannan shekaru hudu masu zuwa. A cewar su, sun nunawa APC goyon-baya a 2019.

KKU KARANTA: An roki Shugaba Buhari ya yi waje da wasu Ministocin da ya yi aiki da su

Eshanumi ta ke cewa cikin mata 360 da su ka nemi takara a zaben da ya gabata, 0.1% ne rak su ka yi nasara a zabe, don haka ta nemi shugaban kasar ya tafi da su a cikin wannan gwamnati mai-ci.

Omorede Osifo-Marshal wanda ta nemi takararar majalisa bana a APC a jihar Edo, ta bayyana cewa su na bukatar rabin kason da ake da su na mukamai a gwamnatin nan ta shugaba Buhari.

Wannan Baiwar Allah ta ke cewa su na so a kara yawan Matan da ke rike da kujerun Ministoci da masu bada shawara da sauran su. Haka zalika Marshal ta na so gwamnoni su yi koyi da hakan.

Ita kuma Ann Agom-Eze, wanda ta yi takarar Sanata a jihar Ebonyi, ta nemi shugaba Buhari ya fito da Ministoci mata daga wasu jihohi da aka bar su a baya domin su fara shirin takarar a 2023.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel