'Yan fashin daji sun hallaka mutane 34 a jihar Zamfara

'Yan fashin daji sun hallaka mutane 34 a jihar Zamfara

A yayin sabunta ta'addanci, wani harin 'yan fashin daji da ya auku a kwana kwanan nan ya salwantar da rayukan kimanin mutane 34 cikin kauyukan Tungar Kafau da kuma Gidan Wawa dake karkashin karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara.

Sai dai wasu mazauan yankin Shinkafi sun ce mutane da aka kashe sun kai 42, inda a ranar aukuwar harin aka samu gawawwakin mutane 40 kuma daga bisani aka tsinto karin gawawwaki na mutane biyu.

Da take bayar da tabbacin aukuwar harin, hukumar 'yan sandan jihar Zamfara ta ce 'yan ta'adda sun tarwatsa mutane ta hanyar harbi na harsashin bindiga kan mai uwa da wabi cikin kauyukan biyu da misalin karfe 5.00 na Yammacin ranar Juma'ar da ta gabata.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Muhammad Shehu yayin gabatar da shaidar sa ga manema labarai, ya ce tuni tarzoma ta lafa a kauyukan biyu na Tungar Kafau da kuma Gidan Wawa, inda kwamishinan 'yan sanda na jihar, Usman Nogogo yayi tattaki wajen kai ziyarar gani da idanu.

KARANTA KUMA: Sojoji 14 sun gurfana da laifin kisa da garkuwa da mutane a Fatakwal

Jaridar BBC Hausa ta bayar da shaidar cewa, wannan ita ce aukuwar hari na baya baya cikin hare-haren 'yan fashin daji da suka addabi jihar Zamfara da kuma sauran jihohi musamman jihar Katsina dake makwabtaka da ita.

A yayin da a halin yanzu wasu mutanen Tungar Kafau da na Gidan Wawa suka nemi mafaka a manyan garuruwa dake ciki da wajen jihar Zamfara, a baya aukuwar wani mummunan hari a kauyen Kanoma da ya janyo salwantar rayuka ya yi sanadiyar dakatar da wani Basarake da kuma hakimi a yanki.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng