Na'Abba, Masari, Dogara da sauran wadanda su ka taba rike Majalisar Wakilai

Na'Abba, Masari, Dogara da sauran wadanda su ka taba rike Majalisar Wakilai

A yau Talata, 11 ga Watan Yuni, 2019, ne Hon. Femi Gbajabiamilla ya zama shugaban majalisar wakilan tarayyar Najeriya. Mun kawo maku jerin sauran Kakakin majalisa da aka yi a kasar nan tun daga 1950s.

1. Fredrick Metcalfe

Sir Fredrick Metcalfe shi ne shugaban majalisar da aka fara yi a tarihi wanda ya rike wannan ofis daga 1955 zuwa 1959. A wancan lokaci Najeriya ba ta samu ‘yancin kai daga Turawan mallaka ba.

2. Jaja Wachukwu

Jaja Wachukwu shi ne wanda ya gaji Fredrick Metcalfe a kan kujerar kakakin majalisar tarayya. Wachukwu ne asalin ‘dan Najeriya na farko da ya fara rike wannan mukami a shekarar 1959.

3. Ibrahim Waziri

Ibrahim Jalo Waziri shi ne wanda ya fi kowa dadewa a kujerar shugaban majalisar wakilai. Waziri ya dare kan wannan mukami ne tun bayan saukan Wachukwu a 1960 har juyin mulkin 1966.

4. Edwin Ume Ezeoke

Sai a lokacin Shehu Shagari ne a ka dawo da majalisa bayan Soji sun mika mulki a Najeriya. Ume Ezeoke ne ya fara rike wannan mukami na shekaru hudu daga 1979 har zuwa shekarar 1983.

5. Chaha Biam

Chaha Biam, mutumin Benuwai shi ne shugaban majalisa a lokacin da Jamhuriya ta biyu ta zarce. Sai dai bayan watanni kadan da kafa gwamnati ne aka hambarar da farar hula a karshen 1983.

KU KARANTA: Abin da ya sa Ndume ya sha kashi a hannun Lawan

6. Salisu Buhari

Rt. Hon. Salisu Buhari, shi ne ya rike mukamin Kakakin majalisa a Najeriya bayan dawowar mulkin farar hula a 1999. Bai dade ba ya yi murabus, ya bar kujerar bisa zargin mallakar satifiket na bogi.

7. Ghali Na’Abba

Wani Mutumin Garin Kano watau Ghali Umar Na’Abba, shi ne ya canji Salisu Buhari a shekarar 2000. Na’Abba ya rike wannan mukami ne har zuwa 2003 lokacin da aka sake yin zabe a Najeriya.

8. Aminu Bello Masari

Rt. Hon. Aminu Bello Masari shi ne Kakakin majalisar tarayya na uku a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo. Masari ya rike wannan mukami ne daga 2003 zuwa 2007.

9. Patricia Etteh

Patricia Olubunmi Foluke Etteh ce ta rike majalisar wakilai a 2007. Sai dai da wuri ta yi murabus tare da Mataimakinta bayan an fara zargin ta da laifin batar da miliyoyi da sunan gyaran gida.

10. Dimeji Bankole

Rt. Hon. Dimeji Bankole ne ya jagorancin ragamar majalisar wakilan Najeriya bayan Patricia Etteh ta sauka. Bankole wanda Matashi ne shakaf ya rike wannan mukami ne har zuwa shekarar 2011.

11. Aminu Tambuwal

Shugaban majalisar wakilan Najeriya daga 2011 zuwa 2015 shi ne Aminu Waziri Tambuwal. Hon. Tambuwal ya rike wannan mukami ne a lokacin wa’adin shugaba Dr. Goodluck Jonathan.

12. Yakubu Dogara

Rt. Yakubu Dogara wanda ya fito daga yankin kudancin Bauchi ne ya zama shugaban majalisar wakilai a 2015. A karshen wa’adinsa, kamar dai Waziri Tambuwal, Dogara ya sauya-sheka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel