Jam’iyyar PDP ta na tare da Ndume da Bago a zaben Majalisa

Jam’iyyar PDP ta na tare da Ndume da Bago a zaben Majalisa

Majalisar NWC ta jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta bayyana matakin da ta dauka a game da zaben sababbin shugabannin ‘yan majalisa da za ayi, kamar yadda mu ka samu labari dazu nan.

A Ranar Talata 11 ga Watan Yuni, 2019, ne Daily Trust ta rahoto cewa jam’iyyar hamayya ta PDP za ta marawa Sanata Ali Ndume da kuma Honarabul Umar Bago baya a zaben majalisar tarayya.

Jam’iyyar ta cin ma wannan mataki ne bayan wani dogon nazari da tayi a cikin ‘yan kwanakin nan, inda ta zauna da masu ruwa-da-tsaki a game da sha’anin majalisa a cikin farkon makon nan.

Sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Umar Ibrahim Tsauri, shi ya bada wannan sanarwa cikin tsakar daren Talata da kimanin karfe 1:30, a wani jawabi da ya fitar a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Manyan PDP sun shiga wani taron gaggawa game da zaben Majalisa

Umar Ibrahim Tsauri yace PDP za su goyi bayan Sanata Mohammed Ali Ndume ne a zaben shugaban majalisar dattawa da za ayi. Sai dai jam’iyyar PDP ce maras rinjaye a majalisar dattawan kasar.

Haka zalika, a majalisar wakilan tarayya, PDP za ta marawa Honarabul Umar Bago baya ne kamar yadda Sakataren jam’iyyar na kasa ya bayyana. Bago ya fito ne daga Jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya.

Wannan mataki da PDP ta dauka ya sabawa umarnin da manyan APC su ka ba ‘ya ‘yan su, inda jam’iyyar mai mulki ta ke so Sanata Ahmad Lawan da Honarabul Femi Gbajabiamila su rike majalisun kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel