Abinda yasa na gudu na bar gidan miji na - Tsohuwar matar gwamnan PDP

Abinda yasa na gudu na bar gidan miji na - Tsohuwar matar gwamnan PDP

A ranar Litinin ne Clara, matar tsohon gwamnan jihar Enugu, Sullivan Chime, ta shaida wa kotu cewar ta gudu ta bar gidan tsohon mijinta ne saboda tsoron kar a raba ta da rayuwar ta.

Matar tsohon gwamnan ta fadi hakan ne yayain da take amsa tambayoyin Paul Onyia, lauyan Chime, a shari'ar neman raba aurensa da Clara da tsohon gwamnan ya shigar a gaban kotu.

"Na sayi motoci guda biyu (Lexus 570 SUV da BMW S6) da kudi na bayan na auri tsohon gwamna Chime," a cewar Clara.

Sannan ta kara da cewa ta sayi wani filaye a Enugu ta hannun hukumar gidaje ta jihar, wadanda ta ce ta biya kudinsu ne bayan mijinta ya bar ofis.

"Ina da takardun kadarorin a wurina har yanzu," ta shaida wa kotu.

Clara na wannan bayani a gaban kotun ne domin kare kanta bayan ta nemi kotun ta umarci tsohon gwamna Chime ya bata rikon 'da daya da suka haifa, sannan ya cigaba biyanta kudin ciyar wa da kula da yaron duk wata.

Kazalika, ta shaida wa kotun cewar tana kasuwancin harkar man fetur da makamashin iskar gas.

Tsohon gwamna Chime ne ya shigar da kara a gaban kotun domin ta raba aurensa da Clara bayan sun shafe shekaru 11 tare.

DUBA WANNAN: Hauwa, matar gwamnan Arewa da ya mutu ta auri matashi mai karancin shekaru (Hotuna)

Saidai, Clara ta shaida wa kotun cewar ba zata amince da bukatar tsohon gwamnan ba a kan raba aurensu ba har sai ya amince cewar zai mika mata rikon 'dan da suka haifa, sannan ya cigaba da biyanta kudin kula wa da shi duk wata.

Clara tayi zargin cewar ba a barinta ta ga yaron ba tare da an saka jami'an tsaro sun mamaye wurin da zata gana da yaron ba.

"Ko da ina gari ba ya bari naga yaro na daya kacal da na haifa a duniya sai a Coci ko wani wurin taro, kuma ko a hakan ma sai tare da jami'an tsaron tsohon gwamnan a wurin," a cewar ta.

Bayan ya kammala sauraren bayanata, alkaliyar kotun, Angela Olatuka, ta daga sauraron cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 14 ga watan Oktoba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel