Zawarci babbar musifa ce – Inji tsohuwar jarumar Kannywood, Hafsat Shehu

Zawarci babbar musifa ce – Inji tsohuwar jarumar Kannywood, Hafsat Shehu

Tsohuwar jarumar Kannywood, Hafsat Shehu ta yi tsokaci akan halin da mata kan shiga idan aka ce suna zawarci.

Hafsat wacce ta kasance mata ga marigayi jarumin Kannywood Ahmed S Nuhu ta bayyana cewa zawarci bala’i da musifa ce domin a cewarta da zaran an kira mace da Bazawara toh shakka babu darajarta da kimarta na raguwa a idanun mutane.

Jarumar tace ya kai har idan aka ce mace bazawara ce sai ka ga kowa yana kaffa-kaffa da ita.

Ta kuma bayyana cewa zaman zawarci na da daci, kuna da kuma cin rai domin a cewarta akwai abubuwan bacin rai a tattare da shi.

Shafin Mikiya na Facebook ya ruwaito inda jarumar ke cewa: “Hakika zawarci bala’i ne, idan mace tana zawarci ta kan shiga halin Ni yasu, darajarta da kimarta raguwa suke, duk inda kace bazawara ce mace to sai kaga ana kaffa-kaffa da ita.

KU KARANTA KUMA: Sabon gwamnan Zamfara ya fantsama cikin daji farautar yan bindiga (Hotuna)

“Zaman zawarci yana da daci da kuna da kuma cin rai, akwai abubuwa da yawa na bacinn rai wanda bazan iya fada ba.”

Mijin jarumar na farko, Ahmed S Nuhu ya rasu ne yan shekarun baya da suka gabata a hanyarsa ta zuwa wajen diramar Sallah da masana'antar kan shirya. Tun bayan rasuwarsa jarumar bata kuma dawowa harkar fim ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel