Jerin sunaye: Sabon gwamnan jihar Gombe ya yi sabbin nade-nade 11

Jerin sunaye: Sabon gwamnan jihar Gombe ya yi sabbin nade-nade 11

Sabon gwamnan jihar Gombe, Muhammad Yahaya Inuwa, ya nada tsohon shugaban jami'ar Maiduguri (UNIMAID), Ibrahim Njodi, a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar Gombe (SSG).

Kazalika, gwamnan ya yi sabbin nade-nade guda 11.

Mohammed Umar, darektan tsare-tsare da harkokin kudi a gidan gwamnati, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Asabar.

Sanarwar ta ce nade-naden da gwamnan ya yi sun hada da shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Gombe, Mohammed Kabir Usman Kukandaka, babban sakatare na musamman ga gwamna (PPS), Usman Mamman Kamara, da kuma babbab mai taimaka wa gwamna a bangare sanarwa da yada labarai, Ismaila Uba Misilli.

Jerin sunaye: Sabon gwamnan jihar Gombe ya yi sabbin nade-nade 11

Muhammad Inuwa Yahaya
Source: UGC

Ragowar nade-naden da sanarwar ta ambata sun hada Kabiru Ibn Mohammad a matsayin mai taimaka wa gwamnna na musamman a bangaren yada labarai, Bintu Aliyu Sunmonu a matsayin mai taimaka wa gwamnna na musamman a bangaren yada labarai, Jack A. Tasha a matsayin mai taimaka wa gwamnna na musamman a bangaren yada labarai.

DUBA WANNAN: Buhari ya goyi bayan kudirin OIC a kan tabbatar da samun 'yancin Falasdinawa

Sai kuma Musa Habibu (Bushasha) a matsayin mai taimaka wa gwamnna na musamman a bangaren tsare-tsare, da Sani Garba a matsayin mai taimaka wa na musamman ga gwamna.

Sanarwar ta kara da cewar ukkan sabbin nade-naden zasu fara aiki ne nan take.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel