Aisha Buhari ta gargadi shugabannin tsaro akan tsare rayukan al'ummar Najeriya

Aisha Buhari ta gargadi shugabannin tsaro akan tsare rayukan al'ummar Najeriya

Duba da yadda lamari na rashin tsaro ke ci gaba da tabarbarewa tare da ta'azzara musamman a Arewacin Najeriya, uwargidan shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari, ta kalubalanci shugabannin tsaro na kasa akan zage dantsen su.

Hajiya Aisha, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Asabar da ta gabata ta nemi shugabannin hukumomin tsaro na kasa da su gaggauta kawo karshen wannan mummunar annoba ta rashin tsaro da yiwa kasar nan dabaibayi.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, mai dakin shugaban kasar Najeriya ta kalubalanci shugabannin hukumomin tsaro na kasar nan da su gaggauta kawo karshen ta'addanci 'yan baranda, hare-haren 'yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran ababe na ta'ada da suka zamto ruwan dare a wasu sassan kasar nan.

KARANTA KUMA: Ministoci da za su dawo a sabuwar Majalisar Buhari

Aisha ta ce dole hukumomin tsaro su mike tsaye wurjajan wajen daukar mataki na fuskantar mummunar ta'adar da zamto karfen kafa a kasar nan ko kuwa a waye gari ba bu kowa a kasar nan yayin da 'yan ta'adda ke shirin karar da al'ummar Najeriya baki daya.

Legit.ng ta fahimci cewa, Aisha ta yi wannan muhimmin kira na kashedi ga hukumomin tsaro yayin bayar da tallafin kayayyaki ga mutane fiye da dubu ashirin da biyar da harin 'yan ta'adda ya auku a kan su cikin jihar Katsina.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel