Rashin Tsaro: Tabbas aminci zai samu a Najeriya - Buhari

Rashin Tsaro: Tabbas aminci zai samu a Najeriya - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin cikin babban birnin kasar nan na tarayya, ya sake bayar da tabbaci na jaddada tsayuwar dakan sa wajen samar da ingantaccen tsaro a fadin kasar nan.

Furucin shugaban kasa Buhari na zuwa ne yayin ganawar sa da kungiyar gwamnonin Arewa cikin babban dakin taro na Council Chambers dake fadar Villa a garin Abuja.

Shugaba Buhari yayin ganawar sa da gwamnonin Arewa

Shugaba Buhari yayin ganawar sa da gwamnonin Arewa
Source: UGC

Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari tare da gwamnonin Arewa sun fara gudanar da ganawar sirrance da misalin karfe 12.30 na ranar Litinin domin tattauna batutuwan da suka shafi kalubale na ci gaba da ta'azzarar rashin tsaro a Arewacin Najeriya.

Bayan sauraron koken gwamnonin Arewa, shugaban kasa Buhari ya sha alwashin share masu hawaye ta hanyar zage dantsen sa wajen tunkarar kalubale na tsaro da suka addabi yankin Arewa kama daga ta'addancin Boko Haram, garkuwa da mutane, rikicin makiyaya da manoma da makamantan su.

KARANTA KUMA: Korafin gwamnoni a kan hukumar NFIU ba ya da tushe - NULGE

Cikin jerin tawagar gwamnonin da suka gana da shugaban kasa Buhari sun hadar da Kashim Shettima (Borno), Nasiru El-Rufa'i (Kaduna), Abdulaziz ABubakar Yari (Zamfara), Muhammad Badaru Abubakar (Jigawa), da kuma Aminu Bello Masari (Katsina).

Sauran gwamnonin sun hadar da Aminu Waziri Tambuwal (Sakkwato), Abubakar Atiku Bagudu (Kebbi), Yahaya Bello (Kogi), Abubakar Sani Bello (Neja) da kuma Simon Bako Lalong (Filato).

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel