Kalli bidiyon yadda yan sanda suka kakkabe maboyar yan bindiga a Katsina

Kalli bidiyon yadda yan sanda suka kakkabe maboyar yan bindiga a Katsina

Wani bidiyo ya billo na jami’an yan sanda a lokacin da suke kakkabe maboyar yan bindiga a yankin karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina.

A cikin bidiyon an nuna yadda jami’an yan sanda suka yi wa sansanin yan ta’addan kawanya bayan sun sha karfinsu.

Yan sandan sun yi wannan nasara ne a atisayarsu ta Operation Puff Adder wanda suka kaddamar akan sansabin yan bindiga da masu garkuwa da mutane a dajin Kogo, da ke karamar hukumar Faskari na jihar.

Rundunar yan sandan ce ta wallafa bidiyon kakkabar a shafinta na twitter inda ta rubuta cewa:

“Atisayar Operation Puff Adder ya dau zafi, ta kai yaki sansanin yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ke dajin Kogo, karamar hukumar Faskari na jihar Katsina.

“Wannan bidiyon na nuna jami’an yan sanda a lokacin da suka kwace ikon sansanin bayan sun sha kan yan bindigan.”

KU KARANTA KUMA: Furuci kan Boko Haram: Gigin tsufa na damun Obasanjo – Dan majalisa Magaji

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, anyi jana’izar mutum 18 da yan bindiga suka kashe a kauyen Yar Gamji da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina a safiyar ranar Laraba, 22 ga watan Mayu a makabartan Dan Takum bayan anyi sallar gawa a fadar sarkin Katsina.

Sarkin Katsina, Abdulmumini Kabir Usman, tare da hakimai da masu rike da sarauta da dama, da kuma jami’an gwamnati na daga cikin daruruwan mutanen da suka halarci jana’izar.

Babban limamin masallacin Juma’a na Katsina, Ustaz Mustapha Ahmed, ne ya jagoranci sallar gawan, yayi addu’a kan Allah ya ji kansu sannan ya ba iyalansu da abokansu juriyar wannan rashi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel