Rundunar Abba Kyari ta samu gagarumar nasara a kan masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja (Hotuna)

Rundunar Abba Kyari ta samu gagarumar nasara a kan masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja (Hotuna)

Tawagar DCP Abba Kyari ta IRT dake karakashin ofishin babban sifeton y'an sanda na kasa (IGP) sun yi nasarar kama wasu gungun barayi da garkuwa da mutane da suka fitini hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Rundinar 'Intelligence Response Team (IRT)' da DCP Abba Kyari jagoranta sun kama wasu masu garkuwa da mutane su tara (9) da suka addabi hanyar Abuja zuwa Kaduna.

An samu miyagun makamai da suka hada da bindiga kirar AK47 guda biyu (2), ma'ajiyar harsashin bindiga guda hudu (4), harsashin bingida guda hamsin da hudu (54), bindiga baushe (Dane gun) guda biyar (5), da kuma shanun sata guda dari biyu (200) a wurin masu garkuwa da mutanen

Sunayen barayin sune kamar haka: Ayuba lawal, Saidu Bello, Abdullahi Bello, Adamu Lawal, da Umar Sani, 'yan asalin karamar hukumar Dan-Musa jihar Katsina, an kamasu ne a cikin jejin Kudaru dake karamar hukumar Lere LGA jihar Kaduna sakamakon bayanan sirri da aka samu daga al'ummar yankin.

Rundunar Abba Kyari ta samu gagarumar nasara a kan masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja (Hotuna)

Masu garkuwa da mutane
Source: Facebook

Rundunar Abba Kyari ta samu gagarumar nasara a kan masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja (Hotuna)

Barayi
Source: Facebook

Rundunar Abba Kyari ta samu gagarumar nasara a kan masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja (Hotuna)

Rundunar Abba Kyari ta samu gagarumar nasara a kan masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja

Sauran barayin sune; Muhammed Sani, Jibrin Shehu, Usman Sani, Musa Garba, an kamasu a cikin jejin Akilbu dake karamar hukumar Kachia jihar Kaduna, masu garkuwa da mutanen sun bada cikakken bayani akan ta'addancin da suka jima suna aikatawa na garkuwa da mutane akan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

DUBA WANNAN: Kotu ta kori karar dan takarar jam'iyyar PDP a Kano

Maigirma shugaban 'Yan sanda ya yabawa al'ummar yankin da suka bada bayanan sirri aka kama wadannan 'yan ta'adda, kuma yana rokon jama'a da su cigaba da bada bayanan sirri da zasu taimaka wajen zakulo miyagun mutane a duk inda suke a boye

Wannan sanarwa ta fito ne daga kakakin rundinar 'yan sandan Nigeria na kasa, DCP Frank Mba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel