Mutanen da su ka tsoma bakin su cikin kan tarkar-tarkar Jihar Kano

Mutanen da su ka tsoma bakin su cikin kan tarkar-tarkar Jihar Kano

Ku na da labari cewa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya raba masarautar kasar Kano. A halin yanzu an samu Sarakuna masu matsayi na daya a cikin Gaya, Rano, Karaye da kuma kasar Bichi a fadin jihar Kano.

Wannan abu ya jawo ce-ce-ku-ce daga mutane da yawa. Legit.ng Hausa ta kawo maku jerin mutanen da su ka nuna rashin goyon bayan su a kan wannan mataki da gwamnan jihar ya dauka.

Daga cikin wadanda su ka nuna rashin amincewar su a kan raba Masarautar Kano akwai:

1. Ibrahim Hassan Dankwambo

Gwamnan Gombe watau Dr. Ibrahim Hassan Dankwambo yayi maza ya fito ya nuna rashin jin dadinsa a kan wannan mataki na gwamnatin Kano. Gwamnan ya fito shafin sa na sada zumunta na Facebook ya rubuta cewa yana tare da Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II.

2. Kingsley Moghalu

Kamar yadda Gwamna Dankwambo yayi magana, Masanin tattalin nan, Kinsgley Moghalu ya fitar da dogon jawabi yana mai sukar kacancana Masarautar da Sarki Muhammadu Sanusi II yake jagoranta. Moghalu yayi takarar shugaban kasa bana a jam’iyyar adawa ta YPP.

KU KARANTA: Mutanen Wudil sun fadawa Ganduje cewa su na tare da Sanusi II

Mutanen da su ka tsoma bakin su cikin kan tarkar-tarkar Jihar Kano

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II yana samun goyon bayan jama'a
Source: Twitter

3. Umar Ardo

Babban jigon jam’iyyar adawa ta PDP, Dr. Umar Ardo, ya fito yayi magana a karshen makon jiya inda yace abin da gwamnatin Kano tayi bai dace ba. Ardo wanda ya nemi tikitin takarar shugaban kasa a PDP a 2015 ya nemi Sarkin Musulmi da sauran Musulmai su tsayawa Sarkin Kano.

4. Ahmad Gumi

Babban Malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi yana cikin wadanda su ka fara yin tir da wannan mataki na kacancana kasar Kano. Dr. Ahmad Gumi yace abin da gwamnan yayi zai kawo rabuwar kai tsakanin Musulmai da su ke bukatar hadin-kan juna a yanzu.

5. Bashir Umar

Shehin Malamin addini kuma Aminin Sarkin Kano, Dr. Bashir Umar ya tofa albarkacin bakinsa a kan wannan takaddama. Babban Malamin yayi wannan magana ne a wajen tafsirin Watan Azumin Ramadan inda yayi kakkausar addu’a ga masu shiryawa Kasar Kano wannan abu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel