Ya dace a canja dukkan shugabanin hukumomin tsaro na Najeriya - ADP

Ya dace a canja dukkan shugabanin hukumomin tsaro na Najeriya - ADP

- Jam'iyyar ADP ta shawarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya canja shugabanin hukumomin tsaro muddin yana son magance matsalar rashin tsaro a kasa

- Shugaban ADP na kasa, Yabagai Yusuf Sani ne ya yi wannnan kirar yayin wata hira da ya yi da manema labarai a babban birnin tarayya, Abuja

- Yabagi ya ce ba zai taba yiwuwa a rika maimaita abu guda ba kuma a rika tsamanin samun sabuwar sakamako

Shugaban jam'iyyar Action Democratic Party (ADP) na kasa, Injiniya Yabagi Yusuf Sani ya shawarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya maye gurbin dukkan shugabanin hukumomin tsaro a Najeriya idan yana son magance kallubalen tsaro a kasar.

A zantawar da Injiiya Sani ya yi da manema labarai a ranar Talata a Abuja, ya ce babu yadda za a samu sauyi a fannin tsaro muddin ba a nada sabbin shugbanin hukumomin tsaro ba.

A canja shugabanin hukumomin tsaro - ADP

A canja shugabanin hukumomin tsaro - ADP
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Kirkirar sabbin masarautu: Mutanen Kano ba za su lamunta ba - Naniya

"A kan batun rashin tsaro, ina tunanin mun san abinda yasa lamarin ya tabarbare. Ba yadda za ayi muyi maimaita abu guda kuma muyi tsamanin sabon sakamako. Babu yadda za ayi ka cigaba da barin tsaffin shugabanin hukumomin tsaro da suka gaza kuma kayi tsamanin za ka samu sabuwar sakamako," inji shi.

"Idan ka samu faduwa a kamfanin ka, za ka cigaba da aiki tare da manajan da aka samu faduwar a karkashin sa?" Sani ya yi tambaya.

Ya cigaba da cewa, "Ya dace shugaba Muhammadu Buhari ya fi kowa sanin cewa karawa jami'an tsaro kwarin gwiwa yana daga cikin abubuwa masu matukar muhimmanci. A matsayin sa na tsohon shugaban mulkin soja, ya san abinda ya dace ya aikata."

Sani ya kuma shawarci hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta saka wasu ka'idoji da jam'iyyun siyasa za su cika kafin a bari su shiga zabe duk da cewa yana goyon bayan siyasar jam'iyyu da yawa.

Ya ce jam'iyyun APC da PDP suna cigaba da mamaye siyasar kasar saboda su ke da gwamnatoci a matakin jihohi da tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel