Daukan doka a hannu: Anyi artabu tsakanin 'yan sanda da 'yan kungiyar sintiri a Katsina

Daukan doka a hannu: Anyi artabu tsakanin 'yan sanda da 'yan kungiyar sintiri a Katsina

'Yan kungiyan sintiri ta vigilante fiye da 1,000 ne suka yiwa ofishin 'yan sanda na karamar hukumar Dandume kawanya inda suke neman a mika musu wasu daga cikin 'yan bindigan da suka kama domin su hallaka su.

Daily Trust ta ruwaito cewa wasu daga cikin wanda ake zargi 'yan bindiga ne sun kai har Unguwar Madugu ne amma sai 'yan sintirin suka ci galaba a kansu kuma suka kama 22 daga cikinsu.

Jim kadan bayan kama shi sai tawagar jami'an 'yan sanda da sojoji suka iso wurin da abin ya faru suka karbe 'yan bindigan suka tafi da su caji ofis.

Daukan doka a hannu: Anyi artabu tsakanin 'yan sanda da 'yan kungiyar sintiri a Katsina
Daukan doka a hannu: Anyi artabu tsakanin 'yan sanda da 'yan kungiyar sintiri a Katsina
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Rashin Tsaro: A haramtawa Buhari fita yawo kasashen duniya - Falana

Sai dai wannan matakin da 'yan sandan suka dauka bai yiwa 'ysn kungiyar sintirin dadi ba hakan ya sa suka garzaya caji ofis din domin su kwato 'yan bindigan su kashe su.

Hakan ya janyo artabu mai zafi tsakanin 'yan sandan da 'yan sai kai inda suka yi musayar wuta.

Haruna, Ja Abdullahi, Shugaban kwamitin mika sauya mulki na karamar hukumar ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce 'yan bindigan sun hana al'ummar garin zuwa sallar Juma'a hakan yasa suka gayyaci jami'an tsaron.

Sai dai kafin jami'an tsaron su iso tuni 'yan kungiyar sintirin sun fafata da 'yan bindigan kuma su kayi nasarar kama wasu daga cikinsu.

A yayin da 'yan sandan suka zo karbar 'yan bindigan, sun ce, "kun san cewa jami'an tsaro ba za su bari al'umma su dauki doka a hannunsu ba. Sannan suka tafi da su zuwa caji ofis na 'yan sanda amma daga bisani 'yan sa kan suka garzaya caji ofis din suka bukaci a mika musu 'yan bindigan su zartas musu da hukunci" inji shi.

Ya cigaba da cewa, babu wanda ya ke barci da idanun sa biyu a cikin 'yan kwanakin nan saboda barazanar kawo hari da 'yan bindigan suke yiwa al'umma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel