Malamai sun ja hankalin El-Rufai a kan kudirin birne matattu

Malamai sun ja hankalin El-Rufai a kan kudirin birne matattu

Majalisar Limamai da Malamai na jihar Kaduna ta bukaci Gwamna Nasir El-Rufai na jihar ya yi watsi da kudirin dokar birne matattu da Majalisar Dokokin Jihar ta mika masa domin neman amincewarsa.

Sakon bayan taro da majalisar ta fitar dauke da sa hannun sakataren ta, Yusuf Yakubu Arrigasiyyu da shugbanta Shaykh Ibrahim Nakaka a jiya a garin Kaduna, ta ce kudirin ya sabawa koyarwan Annabi Muhammadu (SAW).

Malamai sun ja hankalin El-Rufai a kan kudirin birne matattu
Malamai sun ja hankalin El-Rufai a kan kudirin birne matattu
Source: UGC

Cikin abinda kudirin ya kunsa, akwai bukatar, "A yi rajistan jariran da aka haifa a ofishin karamar hukuma kuma a sanar da hukuma idan anyi rasuwa ko an haifi jariri ba bu rai. Jami'an karamar hukumar za su bayar da takardan fom A kafin a bayar da damar birne gawan."

DUBA WANNAN: Bayan cin zabe a PDP, shugaban marasa rinjaye ya koma APC

Majalisar malaman ta kuma bukaci gwamnatin jihar ta gaggauta kawo karshen rikice-rikicen da ake fama da shi a Kajuru da wasu sassan jihar Kaduna.

A wata rahoton, Legit.ng ta ruwaito cewa babban jam'iyyar adawa ta PDP tayi ikirarin cewa tafiye-tafiyen da shugaba Muhammadu Buhari ke yi zuwa kasashen ketare na kara karfafawa masu garkuwa da mutane da sauran 'yan ta'adda tafka barna a kasar.

Jam'iyyar ta PDP tayi kira ga shugbaan kasar ya gaggauta dawowa gida Najeriya domin ya fuskanci kallubalen tsaron da ake fuskanta a sassan kasar daban-daban.

Ta kuma yi ikirarin cewa 'yan ta'addan da ke kaiwa al'umma hari a jihar Katsina baki ne daga kasar Nijar da jam'iyyar APC ta dako haya domin tallafa mata wurin tayar da tarzoma yayin baban zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel