Bafarawa ya zayyana illolin da rashin tsaro ke yiwa tattalin arzikin Najeriya

Bafarawa ya zayyana illolin da rashin tsaro ke yiwa tattalin arzikin Najeriya

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, ya ce matsalar rashin tsaro ta kara zafafa halin kunci da 'yan Najeriya ke ciki saboda barazanar durkusar da tattalin arzikin kasa da matsalar ke yi.

Ya ce sai kowa ya yarda cewar matsalar tsaro ta kowa da kowa ne ba iya gwamnati kadai ba, sannan za a iya samu damar shawo kan ta.

Tsohon gwamnan na wadannan kalamai ne yayin gabatar da wani shiri da zai mayar da hankali wajen tabbatar da zaman lafiya, wanda shine zai dauki nauyin fara shi bayan kammala azumin watan Ramadana a garin Kaduna.

Bafarawa ya zayyana illolin da rashin tsaro ke yiwa tattalin arzikin Najeriya

Bafarawa
Source: Twitter

Bafarawa ya bayyana cewar yawaitar hare-haren kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabas da na 'yan bindiga a yankin arewa maso yamma, ya kashe tattalin arzikin arewacin Najeriya, kuma hakan ya sa masu saka hannun jari basa sha'awar zuwa yankin domin kafa masana'antu ko yin kasuwanci.

DUBA WANNAN: JAMB za ta soke fiye da rabin sakamakon jarrabawa a wasu jihohin Najeriya

Tsohon gwamnan, wanda jigo ne a jam'iyyar PDP, ya ce daga cikin abubuwan da suka haddasa rashin zaman lafiya a Kaduna akwai batun kasancewar APC a matsayin jam'iyyar dake mulkin jihar.

Ya kara da cewa raunin gwamnati ne ya jawo tabarbarewar tattalin arziki da raina dokokin kasa da kuma rashin samun cigaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel