Goje ya dau alwashin kin janyewa daga neman shugabancin majalisa har sai Buhari ya lallashe shi

Goje ya dau alwashin kin janyewa daga neman shugabancin majalisa har sai Buhari ya lallashe shi

Har yanzu tsuguni bata kare a farfajiyar jam’iyyar APC, inda ake ta gumurzu tsakanin wasu manyan Sanatocin jam’iyyar akan wanda zai maye gurbin Sanata mai barin gado, Sanata Bukola Saraki, a matsayin shugaban majalisar dattawa.

Wadannan jiga jigan Sanatocin uku sun hada da shugaban masu rinjaye, Sanata Ahmad Lawan, shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisa, Sanata Danjuma Goje da kuma tsohon shugaban masu rinjaye, Sanata Ali Ndume.

KU KARANTA: Masarautar Machina ta nada gwamnan jahar Yobe wani muhimmin sarauta

Goje ya dau alwashin kin janyewa daga neman shugabancin majalisa har sai Buhari ya lallashe shi
Goje da Buhari
Asali: UGC

Sai dai duk a cikinsu, Ahmad Lawan ne yake samun goyon bayan uwar jam’iyyar APC, dana jagoran APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, dana gwamnonin APC, da kuma na shugaban kasa Muhammadu Buhari, yayinda Goje ke samun goyon bayan Sanatocin jam’iyyar adawa ta PDP.

Legit.ng ta ruwaito sakamakon haka shugaba Buhari ya aika ma Goje da wasu manyan mutane don su shawo kansa ya hakuran ma Ahmad Lawan, daga ciki akwai hadimin Buhari Abba Kyari, Gwamna Kayode Fayemi, Abdul Aziz Yara, Sanata Aliyu Wammako, da Sanata Adamu Aliero.

Sai dai Danjuma Goje ya tubure ya dage kai da fata lallai ba zai janye neman kujerar shugabancin majalisar dattawa ba har sai shugaban kasa Muhammadu Buhari da kansa ya kirashi da kansa ya lallasheshi sa’annan zai hakura.

A yanzu haka ana sa ran wakilan da Buhari ya tura ma Goje zasu shirya wata ganawa tsakaninsa da shugaba Buhari, don ya ji daga bakin Buhari abinda yak enema daga gareshi, kamar yadda ya bukata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel