Kasuwar masu garkuwa da mutane na ci a garin Jalingo

Kasuwar masu garkuwa da mutane na ci a garin Jalingo

- Al'ummar garin Jalingo sun kai kukansu ga hukumar 'yan sanda akan ta kawo musu dauki wurin magance barayin mutane da suka hana su sakat a garin

- Sun bayyana cewa kullum sai an sace mutane 2 zuwa 3 a garin

Mutanen garin Jalingo a jihar Taraba sun yi kira ga shugaban hukumar 'yan sanda na kasa ya aika da dakarun 'yan sanda na musamman zuwa garin Jalingo domin magance matsalar sace-sacen mutane a garin.

A wata hira da aka yi da wani mai fada a ji a garin, Alhaji Usman Habu ya ce, barayin mutanen yanzu ne kasuwar su ta ke ci a fadin yankin.

A cewarsa, kullum sai an sace mutane a garin, sannan kuma kowanne daren Allah sai an sace mutane biyu zuwa uku kafin gari ya waye a garin.

Kasuwar masu garkuwa da mutane na ci a garin Jalingo
Kasuwar masu garkuwa da mutane na ci a garin Jalingo
Asali: Depositphotos

Alhaji ya ce yanzu barayin mutanen suna satar masu kudi ne da manyan ma'aikata. Sannan ya kara da cewa kowanne dare sai sun ji karar harbin bindiga a garin. Ya ce barayin suna amfani da manyan makamai wurin aiwatar da ayyukansu.

Majiyarmu LEGIT.NG ta samu bayanin cewa da karfe 7:30 na dare ya yi zaka nemi mutane ka rasa a fadin garin, saboda tsoron barayin da suka mayar da garin kamar kasuwa.

KU KARANTA: 'Yan gari sun yi fito na fito da 'yan bindiga a jihar Katsina

A cikin 'yan makonnin nan da suka wuce, an sace mutane fiye da 20 a cikin garin, banda wadanda suka sace a wasu sassa na jihar Taraba.

Da yake bayani game da karuwar matsalar barayin a yankin Jalingo, jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar DSP Misal ya ce, hukumar ta na yin iya bakin kokarin ta wurin kawo karshen barayin mutanen dama sauran masu laifuka a yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel