Bidiyon wani mutumi yana cewa Kwankwaso zai masa wankar gawa

Bidiyon wani mutumi yana cewa Kwankwaso zai masa wankar gawa

Mun samu labarin wani Bawan Allah da yake da burin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayi masa wanka a duk lokacin da ya cika. Tsananin soyayyar da yake yi wa ‘dan siyasan ya sa ya dauki wannan matsaya.

Wannan Bawan Allah da ya fito a wani bidiyo yayin da ake yi masa kirarin Kwankwaso, ya bada sako cewa a fadawa babban ‘dan siyasar na jam’iyyar PDP da yayi masa wankar gawa a lokacin da ya bar Duniya.

A wannan bidiyo da wani ya daura a shafin Tuwita kwanaki, an ji wannan mutumi yana cewa a sanar da tsohon gwamnan na Kano ko kuma na-kusa da shi cewa da zarar ya cika, ya taimaka ya masa wanka a bizne sa.

KU KARANTA: Kofa a bude ta ke ga masu sauya-shekar siyasa a Kano

Bidiyon wani mutumi yana cewa Kwankwaso zai masa wankar gawa
Dan Kwankwasiyya yana so Sanatan na Kano ta tsakiya yayi masa janaza
Asali: Depositphotos

Saboda ‘dan karen soyayyar da wannan Mutumi yake yi wa Sanatan na jihar Kano, ya roki yayi masa sallar jana’iza bayan yayi masa wanka. Bisa dukkan alamu dai wannan mutumi ya karbi darikar Kwankwasiyya.

Wannan mutumi mai dauke da hular Kwankwasiyya ya nemi ‘dan siyasar ya wakilta wani mutumi yayi masa wankar gawa idan har shi ba zai samu lokaci ba. Amma yake cewa sam bai daukewa ‘dan siyasar yi masa sallah ba.

Na kusa da wannan mutumi dai sun ce za su zura idanu domin ganin ranar da ‘Yan Kwankwasiyya za su yi masa sutura, sannan kuma Madugun na Kwankwasiyya ya shige gaba ayi masa jana’iza.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel