Tsaka mai wuya: Kotu ta karbi sabbin shaidu a kan tuhumar da EFCC ke wa Nyako

Tsaka mai wuya: Kotu ta karbi sabbin shaidu a kan tuhumar da EFCC ke wa Nyako

Wata kotun gwamnatin tarayya dake zamanta a Abuja ta karbi karin wasu takardu a matsayin shaida da Mista Chris Odofi, shaida na 20 da aka gabatar a gaban kotun, ya gabatar a cigaba da tuhumar zargin badakalar biliyan N29 da ake yiwa tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar an gurfanar da Nyako tare da dan sa, Sanata Abdul-Aziz Nyaki, da Abubaka Aliyu da Zulkifikk Abba bisa tuhumar su da hada baki domin aikata sata, cin amanar aiki da safarar kudi.

Daga cikin takardun da kotun ta karba akwai na wasu kamfanoni biyu; 'Blue Opal Nigeria Limited' da 'Blue Opal Sales Details'.

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arzikin kasa (EFCC) ce ta gurfanar da Nyako da dan sa, Sanata Abdul-Aziz, tare da ragowar mutane biyu.

Tsaka mai wuya: Kotu ta karbi sabbin shaidu a kan tuhumar da EFCC ke wa Nyako
Murtala Nyako
Source: Twitter

An gurfanar da Nyako da ragowar mutanen tare da wasu kamfanonin biyar; Blue Opal Limited, Sebore Farms & Extension Limited, Pagoda Fortunes Limited, Tower Assets Management Limited da Crust Energy.

Mista Rotimi Jacob, babban lauya mai lambar SAN, ne ya gabatar da shaidar tare da yi masa tambayoyi a gaban kotun.

DUBA WANNAN: 'Yan daba sun datse hannayen wani dalibin jami'ar Usman Danfodiyo, hotuna

Sai dai, Mista Ibrahim Isiaku, lauyan dake kara wadanda ake tuhuma, ya roki kotu ta daga sauraron karar domin su yi nazarin shaidun da Mista Odofin ya gabatar a gaban kotun.

Alkalin kotun, Jastis Okon Abang, ya daga sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Afrilu domin lauyan dake kare wadanda ake kara ya gabatar da tambayoyi ga Odofin. (NAN).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel