An kori diyar 'dan majalisar tarayya da aka gano tana aiki da takardun bogi

An kori diyar 'dan majalisar tarayya da aka gano tana aiki da takardun bogi

- An kori diyar wata dan majalisa bayan an gano tana amfanin da takardan kammala makaranta na bogi ne a wurin aiki

- Rahotani sun ce Deborah Agbonayinma tana aiki ne da Hukumar Fansho na Kasa (PenCom) da takardun bogi na makarantun Najeriya da kasashen waje

- Agbonayinma diyar dan majalisar tarayya ne mai wakiltan mazabar Egor/Ikpoba-Okha a jihar Edo

Deborah Ighiwiyisi Agbonayinma diyar dan majalisar dokokin tarayya kuma shugaban kwamitin fansho na majalisar wakilai, Ehionzuwa Johnson Agbonayinma ta rasa aikinta bisa zargin da ake yi na cewa takardun bogi ta ke amfani da shi.

A cewar rahoton da The Nation ta wallafa, An kori Agbonayinma daga Hukumar Fansho na Kasa (PenCom) inda ta kwashe shekaru uku tana aiki bayan an gano takardun karatun da ta gabatar na kammala jami'a a Najeriya da kasar waje duk na bogi ne.

DUBA WANNAN: Wata mata ta fadi matacciya yayin fada da kishiya a Kano

An kori diyar 'dan majalisar tarayya da aka gano tana aiki da takardun bogi
An kori diyar 'dan majalisar tarayya da aka gano tana aiki da takardun bogi
Asali: UGC

Takardan neman aiki da Agbonayinma ta gabatarwa PenCom a lokacin da za a dauke ta aike ya nuna cewa tayi karatun digiri a fanin Akanta da ta kammala a ranar 8 ga watan Augustan 2012 daga Irish University Business School da ke 219 Bow Road, London E3 2SJ.

Sai dai a lokacin da wata kwamitin bincike a PenCom ta bincika sai ta gano babu wata jami'a mai bayar da digiri a Landan mai wannan sunan.

Kwamitin ya ce: "Munyi bincika a shafin intanet na gwamnatin kasar Ingila kuma sunan jami'an baya cikin makarantun da aka amince su rika bayar da digiri."

Bayan kwamitin ta ki karbar satifiket din da Agbonayinma ta kawo daga Ingila saboda na bogi ne, an ce ta sake gabatar da wani shaidan digiri din daga Jami'ar Olabisi Onanbanjo na jihar Ogun sai dai shima daga baya an gano na bogi ne.

Dan majalisar tarayyar ya ki cewa uffan a kan lamarin a yayin da manema labarai suke nemi jin ta bakinsa a kan halin da diyarsa ke ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel