Masu zuwa neman maganin Bindiga a Zamfara 19 sunyi hatsari sun mutu

Masu zuwa neman maganin Bindiga a Zamfara 19 sunyi hatsari sun mutu

Mutane goma sha tara ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin mota da ya faru da su a Daudawa da ke karamar hukumar Faskari na jihar Katsina a kan hanyarsu na dawowa daga kauyen Kauran Tsauni da ke gundumar 'Yan Kuzo a karamar hukumar Tsafe na Jihar Zamfara domin shan maganin bindiga.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura, FRSC na shiyar Funtuwa, Joshua Bulus Ako ya tabbatar da afkuwar wannan hadarin tare da mutuwar mutum 19 da kuma 38 kwance a asibitin karamar hukumar Funtua suna karbar magani.

Joshua Bulus ya kara da cewa, "Hadarin ya faru ne misalin karfe bakwai na safiyar Juma'a a Daudawa cikin karamar hukumar Faskari mai nisan kilomita 15 tsakanin garin da karamar hukumar Funtua."

DUBA WANNAN: Jerin sunayen sojojin Najeriya da ISWA ta hallaka

Masu zuwa neman maganin Bindiga a Zamfara 19 sunyi hatsari sun mutu
Masu zuwa neman maganin Bindiga a Zamfara 19 sunyi hatsari sun mutu
Asali: Original

Ya ce, sun garzaya wurin da hadarin ya afku jim kadan bayan faruwarsa inda suka dauko wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Funtua.

Bayanai sun nuna cewa hadarin ya faru ne sakamakon bacci da direban motan keyi tare da gudu da ya wuce kima. Motar kirar Mitsubishi Kanta mai lamba DK 654 ZP na dauke da fasinjoji 60 ne a lokacin da wannan mummunan hadarin ya faru, a cewar Joshua.

Kwamandan na FRSC ya nuna damuwarsa a kan yadda ake daukan fasinjoji fiye da ka'ida a cikin motocci wanda hakan ke sanadiyar salwantar rayukan al'umma da dama. Ya shawarci direbobi su rika bin dokokin tuki da tafiya cikin natsuwa.

Wani daga cikin fasinjojin da hadarin ya ritsa da shi mai suna Buhari Usman Gani ya bayyanawa Leadership cewa sun fito ne daga karamar hukumar Rafi cikin jihar Neja kuma dukkansu 'yan kungiyar sa-kai ne, "mun tafi Tsafe ne domin shawo maganin Bindiga kuma a hanyar mu ta dawowa ne hadarin ya faru."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel