Buba Galadima ya bayyana irin dangantakar da ke tsakanin 'yarshi da shugaba Buhari

Buba Galadima ya bayyana irin dangantakar da ke tsakanin 'yarshi da shugaba Buhari

- Ya bayyana 'yar tashi a matsayin wacce tafi kowa ilimi a majalisar shugaba Buhari

- Ya bayyana cewa an kuma yi wa kwamishinan 'yan sandan jihar Kano korar dole a lokacin da za a sake zaben gwamna karo na biyu

- Ya kara da cewa aakwai shaidu da suke nuna cewa Atiku ne ya lashe zabe

Buba Galadima, ya ce ya na mamakin yadda aka yi ba a bawa diyarshi babban mukami ba a majalisar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa diyar tashi ta na da dangantaka mai karfi da shugaban kasar.

A wata tattauna da ya yi da manema labarai, ya ce rikicin siyasa da tashin-tashina da aka yi a lokacin zaben gwamnan jihar Kano karo na biyu, ya faru ne dalilin hana kwamishinan 'yan sanda tabuka komai a jihar.

Buba Galadima ya bayyana irin dangantakar da ke tsakanin 'yarshi da shugaba Buhari
Buba Galadima ya bayyana irin dangantakar da ke tsakanin 'yarshi da shugaba Buhari
Asali: UGC

A cewar shi: "Wadanda su ke cewa diyata ta na aiki da shugaba Buhari, su na yi mini ba'a ne. 'Diyata kamar diya ce a wurin shugaba Buhari, saboda a al'ada duk wanda ya yi wa mace walittaka kamar uba ne ga wannan yarinyar. 'Ya ta tana da tarihi da shugaba Buhari. Ko lokacin da ta gama karatun ta a birnin Landan, ni da Buhari muka je mata bikin yaye dalibai; lokacin da za ayi aurenta, Buhari ne ya yi mata walicci. Lokacin da ta haihu dan ta na farko sunan Buhari ta saka mishi.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta tarawa Najeriya biliyan N251 a cikin watanni 16

"Sannan kuma diyata cikakkiyar 'yar Najeriya ce, ta yi aiki da mataimakin shugaban kasa tukuru domin ganin shugaba Buhari ya hau mulki, a takaice ma ita ce wacce ta jagoranci kamfen din shi a birnin tarayya. A ga ni na idan za a biya ta da irin wahalar da ta yi, kamata ya yi a bata matsayin minista. Diyata ta na da kwalin digiri guda biyu, da kuma kwaalin digirin-digirgir guda uku.

"Babu wani mutum a cikin 'yan majalisar Buhari da ya ke da irin takardun ta, hatta shi shugaban kasar. Amma kuma duk da haka an hana ta wani babban mukami."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel