Ran maza ya baci - Hotunan Abba Kyari a lokacin da yake neman masu garkuwa da mutane a dajin Kaduna

Ran maza ya baci - Hotunan Abba Kyari a lokacin da yake neman masu garkuwa da mutane a dajin Kaduna

Babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna ta zama matattarar 'yan fashi da masu garkuwa da mutane, inda mutane da dama suke tsoron bin hanyar sanadiyyar kama mutane da 'yan garkuwa da mutane suke yi.

Ran maza ya baci - Hotunan Abba Kyari a lokacin da yake neman masu garkuwa da mutane a dajin Kaduna

Ran maza ya baci - Hotunan Abba Kyari a lokacin da yake neman masu garkuwa da mutane a dajin Kaduna
Source: Facebook

Hakanne ma ya sanya hazikin dan sandan nan Abba Kyari tare da tawagar sa suka shiga dajin dake kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna din domin kama masu garkuwa da mutanen, akwai yiwuwar shigar Abba Kyari dajin zai iya sanyawa a samu saukin 'yan ta'addar da suke damun al'umma, saboda ganin irin hazakar da dan sandan yake da ita.

Ran maza ya baci - Hotunan Abba Kyari a lokacin da yake neman masu garkuwa da mutane a dajin Kaduna

Abba Kyari da tawagar sa lokacin da suka shiga cikin dajin Kaduna
Source: Facebook

Idan ba a manta ba a jiya Laraba 3 ga watan Afrilu, majiyarmu LEGIT.NG ta kawo muku yadda gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai da tawagar sa suka tarwatsa wasu 'yan ta'adda da suka yi kokarin garkuwa da matafiya akan hanyar ta Abuja zuwa Kaduna.

Ran maza ya baci - Hotunan Abba Kyari a lokacin da yake neman masu garkuwa da mutane a dajin Kaduna

Abba Kyari yana gabatar da bincike akan wani mutum
Source: Facebook

Rahoton hakan ya fito daga bakin wani na hannun daman gwamnan Samuel Aruwan, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai.

Aruwan ya bayyana cewa, a lokacin da suke kan hanyar su ta zuwa Abuja, gwamnan ya yi kicibus da motoci a tsaye akan hanya, kusa da kauyen Akilubu, da misalin karfe 3:40 na yammma. Ya kara da cewa mazauna kauyen sun bayyana cewa akwai masu garkuwa da mutane da suka tare hanyar.

KU KARANTA: Yadda mijina ya gamu da ajalinshi a garin yi wa ma'aurata sulhu

Ran maza ya baci - Hotunan Abba Kyari a lokacin da yake neman masu garkuwa da mutane a dajin Kaduna

Ran maza ya baci - Hotunan Abba Kyari a lokacin da yake neman masu garkuwa da mutane a dajin Kaduna
Source: Facebook

A sanarwar ta sa ya bayyana ce wa: "Jami'an tsaron da suke tawagar gwamnan sune suka je suka kori 'yan ta'addar, suka arce cikin daji.

"Bayan tawagar ta kori 'yan ta'addar, gwamnan ya bada umarnin a dauki mutanen da 'yan ta'addar suka yi wa rauni a kai su asibiti mafi kusa.

"Sannan gwamnan ya bukaci jami'an tsaro su, tsaya domin tabbatar da hanyar ta yi lafiya ga matafiya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel