Akwai ayar tambaya a zaben jihohin Adamawa, Bauchi da Sokoto - APC

Akwai ayar tambaya a zaben jihohin Adamawa, Bauchi da Sokoto - APC

Mataimakin sakataren yada labaran jam'iyyar APC na kasa, Mista Yekini Nabena, ya ce akwai babbar ayar tambaya a kan zabukan kece raini da aka gudanar a jihohin Adamawa, Bauchi da Sokoto.

Ya ce zabukan da aka gudanar a jihohin basu da cikakken sahihanci.

Nabena ya bayyana hakan ne yayin wata hira da 'yan jarida a Abuja, a yau, Alhamis.

Jam'iyyar adawa ta PDP ce ta lashe zaben gwamna a jihohi ukun da Nabena ke korafi a kansu.

Aminu Waziri Tambuwa ya yi tazarce a jihar Sokoto, Bala Muhammed ya kayar da gwamnan APC mai ci a jihar Bauchi, kamar yadda Ahmadu Finitiri ya yi a jihar Adamawa.

Nabena ya nuna rashin gamsuwar sa a kan yadda jam'iyyar PDP tayi nasara a jihohin, tare da bayyana cewar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ba ta gudanar da zabe a jihohin bisa dokokin hukumar ba.

Akwai ayar tambaya a zaben jihohin Adamawa, Bauchi da Sokoto - APC
Yekini Nabena
Asali: Twitter

Ya yi zargin cewar an tafka magudi da sayen kuri'a da amfani da 'yan ta'adda yayin zabukan da INEC ta maimaita a jihohin uku.

"Bayan mun yi bitar zaben da aka maimaita a jihohin Adamawa, Bauchi da Sokoto, mun tabbatar da cewar an tafka magudi, an sayi kuri'a kuma an yi amfani da 'yan daba.

DUBA WANNAN: Yadda za a raba arewa da kungurmin talauci - Aliko Dangote

"Jam'iyyar APC keda rinjayen a majalisar dokokin jihohin Bauchi da Sokot a zaben farko da aka gudanar, amma saboda an tafka magudi tare da rashin yin amfani da dokokin zabe da INEC tayi, mun rasa kujerun gwamna bayan an maimaita zaben a zagaye na biyu," a cewar Nabena.

Banena ya kara da cewar yana da karfin gwuiwar APC zata karbi kujerun gwamna a jihohin a gaban kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel