Yanda haduwa ta da Leah Sharibu ta kasance a sansanin 'yan Boko Haram - Wata Budurwa data sha da kyar

Yanda haduwa ta da Leah Sharibu ta kasance a sansanin 'yan Boko Haram - Wata Budurwa data sha da kyar

- A shekarar data gabata ne dai 'yan ta'addar Boko Haram suka yi garkuwa da dalibai sama da 100, a makarantar sakandare dake garin Dapchi, dake cikin jihar Yobe

- 'Yan ta'addar sun saki sauran daliban inda suka rike daya daga cikin daliban, saboda taki komawa addinin Musulunci

- Wata budurwar wacce ta sha da kyar ta bayyana yanda haduwar su ta kasance da dalibar a sansanin 'yan ta'addar dake cikin dajin Sambisa

Yanda haduwa ta da Leah Sharibu ta kasance a sansanin 'yan Boko Haram
Yanda haduwa ta da Leah Sharibu ta kasance a sansanin 'yan Boko Haram
Asali: Depositphotos

Wata budurwa, wacce ta sha da kyar daga hannun 'yan Boko Haram, ta bayyanawa wasu 'yan jarida, yanda haduwar ta da Leah Sharibu ta kasance a sansanin 'yan Boko Haram, dake cikin dajin Sambisa. Sannan matar ta bayyana yanda wasu mata da jarirai guda takwas suka rasa rayukan su, a lokacin da suke kokarin guduwa daga sansanin 'yan Boko Haram din.

Budurwar mai shekaru 25 ta bayyana sunan ta da Ruth, tace tun lokacin da 'yan ta'addar suka kama ta, shekaru biyar da suka wuce, tace sun tilasta ta akan ta bar addinin ta na Kiristanci ta koma addinin Musulunci.

KU KARANTA: PDP zata ja daga idan ba'a baiwa Abba Kabir Gwamnan jihar Kano ba

Tace a lokacin da take zaune a sansanin 'yan Boko Haram, an sha hada su daki daya da Leah Sharibu, dalibar da 'yan Boko Haram suka yi garkuwa da ita tare da wasu dalibai fiye da 100, a makarantar sakandare dake Dapchi, dake jihar Yobe.

Yayinda 'yan ta'addar sun saki sauran daliban da sukayi garkuwa dasu, ita kuwa Leah Sharibu har ya zuwa wannan lokaci tana hannun su, dalilin taki ta bar addinin ta na Kiristanci ta koma addinin Musulunci.

Ruthe tace ta gudu ta bar Leah Sharibu a sansanin na 'yan ta'addar, inda take yin wa'azi tare da warkar da marasa lafiya. Ta kara da cewa ta taba yin ciwon ciki mai tsanani, inda da taimakon Leah ta samu sauki.

Tace 'yan ta'addar sun tilasta ta, ta dinga kwanciya da daya daga cikin su, inda daga baya suka yi mata auren dole da shi mutumin.

Tace bayan sun samu damar kubuta daga hannun 'yan ta'addar sai da suka shafe sama da kwana 90 suna yawo a cikin daji, babu abinci, sai dai su dinga cin ganye.

Ta kara da cewa a kokarin su na neman tsira daga hannun 'yan ta'addar ne, wasu mata su takwas tare da jariran su suka rasa rayukan su. Inda dole suka dinga tsallake gawarwakin su suna barin su a dajin ba tare da sun rufe ba.

Ruth tace, sun samu sun kubuta ne ita da danta, bayan da wasu sojoji suka kawo musu dauki, a can cikin wani daji, cikin jihar Gombe.

Ta kara da cewa ta rasa iyayenta tun kafin 'yan ta'addar su sace ta, sannan akan idon ta aka yiwa 'yan uwanta yankan rago, duk saboda sunki barin addinin su na Kiristanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel