Har yanzu muna tattaunawa da wadanda ke garkuwa da Sheikh Sulaiman - Iyalansa

Har yanzu muna tattaunawa da wadanda ke garkuwa da Sheikh Sulaiman - Iyalansa

Iyalan shahararren mahadacin Al-Kura'ani mai girma dan jihar Kano, Sheikh Ahmad Sulaiman sun ce har yanzu suna tattaunawa da wadanda su kayi garkuwa da shi a kan kudin fansa da suke son a biya kafin a sako shi.

Da ya ke magana a madadin iyalan malamin, Malam Muhammad Kabir ya ce har yanzu ana cigaba da tattaunawa tsakanin iyalan malamin da wadanda suke rike da shi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Har yanzu muna tattaunawa da wadanda ke garkuwa da Sheikh Sulaiman - Iyalansa
Har yanzu muna tattaunawa da wadanda ke garkuwa da Sheikh Sulaiman - Iyalansa
Asali: Twitter

Ya ce, "Har yanzu ba mu cimma matsaya ba, saboda haka ba zan iya fadin adadin kudin da masu garkuwa da shi ke bukata daga iyalansa ba amma dai akwai alamun nasara a lamarin.

"Ina son in tabbatarwa dukkan al'ummar musulmi cewa Sheikh Sulaiman yana cikin koshin lafiya kuma muna fata za a sako shi nan da kankanin lokaci."

DUBA WANNAN: Buhari ya yi watsi da wasu kudiri 5 da majalisa ta amince da su

Ya kuma bukaci dukkan al'ummar musulmin Najeriya su taimakawa malamin da addu'a, inda ya ce babu wata tsanani da addu'a ba za ta iya warware wa ba.

Idan ba a manta ba dai wasu 'yan bindiga ne suka sace Sheikh Suleiman ne tare da wasu malaman addinin musulunci biyar a ranar Juma'a da ta gabata a hanyar Sheme zuwa Kankara na jihar Katsina a hanyarsu na komawa Kano bayan sun baro birnin Kebbi.

A baya, Legit.ng ta kawo muku cewa malamin ya aike da sako a hirar inda ya roki al'ummar musulmi su taimaka masa domin rayuwarsa na cikin hadari.

A wani labarin kuma Shugaban 'yan bindigan da suka yi garkuwa da fitaccen mahaddacin Al-Qur’anin nan, Sheikh Ahmad Sulaiman ya bayyana cewa wani babban dan siyasa daga jahar Kebbi ne ya biyasu donsu halaka shi, inda yace naira miliyan dari uku ya biyasu.

Shugaban 'yan bindigan ya bayyana haka ne cikin wani hira da yayi da wani aminin Malamin ta wayar tarho, inda ya nemi sai an biyasu akalla naira miliyan 300, da kuma kudin man da suka kona kafin su saki Alaramma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel