Maza na daf da kare wa a duniya – Binciken kimiyya

Maza na daf da kare wa a duniya – Binciken kimiyya

Wata jami’ar kasar Ingila dake garin Kent ta bayyana cewar ta gudanar da wani bincike dake nuna cewar nan bada dadewa ba maza zasu kare, su gushe daga doron kasa tamkar ba a taba halittar su ba.

Kwararren masanin kimiyya jami’ar Kent, Darren Griffin, ya bayyana cewar maza zasu kare ne saboda kwayar halittar Y, dake rikidewa zuwa namiji yayin haduwar maniyyin mace da namiji lokacin daukar ciki, zai kare, wanda hakan daidai yake da gushewar maza daga doron kasa.

Batun lamarin karewar kwayar halittar Y dake cikin maniyyi na cigaba da tayar da hankulan masu bincike a bangaren kimiyya musamman ganin cewar kwayar halittar day ace tal a jikin mutum kuma babu madadin ta.

Maza na daf da kare wa a duniya – Binciken kimiyya
Ma su binciken kimiyya
Asali: UGC

Masana sun bayyana cewar daga cikin abubuwan da zasu jawo karewar kwayar halittar Y a jikin bil’adama akwai kwankwadar barasa (giya) dake hana kwayar ta cigaba da haihuwa na tsawon shekaru kamar yadda ragowar kwayoyin halitta ke haihuwa da sabunta kan su.

DUBA WANNAN: Ba zan saka baki a zabukan da za a maimaita ba – Sakon Buhari ga APC

Wannan dalilin ne yasa Griffin bayyana cewar akwai yiwuwar karewar kwayar halittar Y gaba daya a doron kasa.

Sakamakon binciken na Griffin ya saka masana da ma su nazari yin tambayar ko yaya rayuwa zata kasance idan babu maza a duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel