Rikicin PDP: Abba Yusuf yayi nasara a Kotun daukaka kara a kan Jafar Bello

Rikicin PDP: Abba Yusuf yayi nasara a Kotun daukaka kara a kan Jafar Bello

Babban kotun daukaka kara da ke cikin Garin Kaduna, ta tabbatar da takarar Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin cikakken wanda ke rike da tutar jam’iyyar PDP mai adawa a zaben gwamna na Kano.

Rikicin PDP: Abba Yusuf yayi nasara a Kotun daukaka kara a kan Jafar Bello
Kotu tace Surukin Kwankwaso watau Abba Yusuf ne 'Dan takarar PDP
Asali: UGC

Kotun da ke zama a Kaduna, ta yanke hukunci cewa Abba Yusuf shi ne ainihin ‘dan takarar PDP na gwamna a zaben jihar Kano na bana. Babban Alkalin wannan kotun ya tabbatar da hukuncin Alkali A. T Badamasi yayai a baya.

Alkali mai shari’a ya bayyana cewa karar da Jafar Sani Bello, wanda yana cikin masu neman kujerar gwamnan jihar Kano, ya kai sake shigar da kara gaban kotu yana kalubalantar tikitin da PDP ta ba Injiniya Abba K. Yusuf.

KU KARANTA: Malamin addini Sheikh Gumi yayi magana kan zaben Kano da za a karasa

Duk Alkalan da ke zama a Kotun daukaka karar na Kaduna sun yi watsi da karar da aka kawo masu inda su kace kukan da Jafar Bello yake yi bai da tushe. Kotun tace babu wata hujjar rushe hukuncin da karamar kotu tayi.

Jafar Sani Bello yana so ne kotun ta bayyana sa a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwani na gwamnan Kano a karkashin PDP a madadin Abba Yusuf wanda suruki ne wurin tsohon Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso.

Lauyan Abba Yusuf watau Bashir Yusuf Tudun Wazirci ya ji dadin yadda aka yi fatali da karar Sani Bello. Shi kuma kakakin yakin neman zaben Yusuf watau Sanusi Bature Dawakin-Tofa, yace hakan ya nuna alamun nasara na kusa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel