Abin kunya: Uwa ta tona asirin mijinta da ke kwanciya da yaransu

Abin kunya: Uwa ta tona asirin mijinta da ke kwanciya da yaransu

Wata 'yar kasuwa mai shekaru 63, Mabel Ali ta roki wata kotu da ke zamanta a Igando ta raba aurenta da mijinta Richard wanda ta yi ikirarin yana saduwa da yaransu kuma har ya yiwa kanwanta ciki.

Ta shaidawa kotu cewa mijinta ya yi lalata da dukkan 'ya'yansu mata uku kuma duk da haka yana neman mata a waje.

Miji na yana saduwa da yaranmu uku - Uwargida ta shaidawa kotu
Miji na yana saduwa da yaranmu uku - Uwargida ta shaidawa kotu
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Tirkashi: An nada Dino Melaye da Ortom wakilan zabe a zaben gwamna da za a maimaita

"Bayan ya yiwa kanwa ta ciki, ya dauki daya daga cikin diyarmu ya kai ta asibiti domin a zubar mata da ciki.

"Diya ta mai shekaru 13 ta fada min cewa ya kan sulala ya shiga dakinta cikin dare ya yi lalata da ita.

"Na sha kama miji na turmi da tabarya tare da diyar mu ta uku. Bai kyale kawaye na da masu aikin gida ba, na kama shi da su," matar tayi ikirari.

Mai shigar da karar kuma ta ce mijin matsafi ne kuma yana son ya yi amfani da ita domin ayi masa asiri ya yi arziki ya yi amfani da kudin domin siyasarsa.

"Ya kai ni wurin 'yan tsibbu da dama a Badagry, Sango da wasu wurare; na biye masa mun tafi saboda ya ce min neman sa'a za mu tafi.

"Na daina binsa bayan daya daga cikin 'yan tsibbun da muka ziyarta ya fada min in dawo in gan shi tare da diya ta.

"Ya fada min in dena bin mijina in san yadda zan kwaci kaina saboda mijina yana son ya yi amfani da ni ya yi asiri ko ya haukatar da ni domin ya ci gadon kadarori na da suka hada da motocci da gidaje.

"Mijina yana karbar kudi daga hannu na yana kashewa wurin yin asiri domin siyarsa sa amma daga baya bai yi nasarar ba.

Mabel ta ce mijinta baya kula da yaransu saboda haka ta roki kotu ta raba aurensu.

Sai dai Richard ya musunta dukkan zargin da matarsa tayi a kansa amma ya amince da bukatar ta na raba aurensu inda shima ya ce baya sha'awan cigaba da zama da ita.

Ya yi ikirarin cewa shine sanadin arzikin matarsa.

Bayan sauraron dukkan bangarorin biyu, shugaban kotun, Mr Adeniyi Koledoye ya daga cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 2 ga watan Mayu domin yanke hukunci kamar yadda NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel