Zaben Kano: INEC ta ja kunnen masu yada sakamakon zaben Gwamna da Majalisar Dokoki

Zaben Kano: INEC ta ja kunnen masu yada sakamakon zaben Gwamna da Majalisar Dokoki

Hukumar zabe na kasa mai zaman-ta watau INEC tayi watsi da sakamakon zaben da wani Hadimin gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya rika saki a jiya Asabar bayan an kammala zabe.

A jiya ne dai aka yi zaben gwamna da ‘yan majalisar dokoki a jihar Kano inda wani daga cikin mai ba gwamnan jihar Kano shawara watau Malam Uba Danzainab ya rika fitar da sakamakon zaben da aka yi a wasu rumfuna a jihar.

Danzainab yayi ikirarin cewa gwamna mai-ci Abdullahi Ganduje ne yake samun nasara a jam’iyyar APC inda yake lallasa ‘dan takarar PDP watau Abba Yusuf. Sai dai hukumar ta INEC ta bayyana cewa ba hurumin Hadimin bane.

Hukumar INEC ta ja kunnen Uba Danzainab da duk wani mai alkaluman kuri’un da aka kada cewa bai halatta wani da ba hukuma ba ya zama yana sanar jama’a sakamakon zaben da aka yi. INEC tace wannan ya sabawa doka.

KU KARANTA: Tsohon Gwamna Shekarau ya rasa rumfunan zaben sa a Kano

Zaben Kano: INEC ta ja kunnen masu yada sakamakon zaben Gwamna da Majalisar Dokoki
INEC ta gargadi masu fesa sakamakon zaben Gwamna a Kano
Asali: Depositphotos

INEC tayi wannan jawabi ne ta bakin babban kwamishinan zabe na jihar watau Riskuwa Arabu-Shehu. Babban jami’in na INEC yace kawo wannan lokaci ana cigaba da kirga kuri’u ne a Gundumomi da kuma cikin kananan hukumomi.

A dokar zaben Najeriya na 2010, Malaman INEC ne kurum ya halatta su tattara kuri’u, sannan kuma su kididdiga har su fadi sakamakon zaben da aka yi. Duk wanda aka samu yana shiga hurumin da ba na sa ba zai yabawa aya zakin ta.

Jam’iyyar PDP ita kuma ta bakin Sanusi Dawakin Tofa wanda shi ne yake magana a madadin ‘dan takarar ta, Abba Yusuf, ya nemi jami’an tsaro su yi maza su yu ram da Hadimin Gwamnan da yake cewa APC ta ci zabe a Garuruwa 13.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel