Jaruma Hadiza Gabon ta bayar da agajin N500,000 ga marar lafiya

Jaruma Hadiza Gabon ta bayar da agajin N500,000 ga marar lafiya

Fitaciyar jurumar Kannywood Hadiza Gabon ta bayar da gudunmawar zunzurutun kudi N500,000 ga mai shirya fina-finai Rabiu Arrahus da za a yiwa tiyata bayan hadarin mota da ya rutsa da shi.

Jarumar wadda sauran abokan aikinta suka rika sanya wa albarka a kafafen sada zumunta ta kasance tana gudanar da ayyukan tallafawa al'umma a jihar Kano da sauran jihohin Arewa tun a baya.

Shahararen dan wasa kuma mawaki na Kannywood, Tamam Sha'aban ya wallafa wani rubutu a shafin sada zumunta a farkon wannan makon inda ya bayyana cewa abokin aikinsu ya yi hadari kuma za ayi masa tiyata.

DUBA WANNAN: Dan takarar APC da ya fadi zaben kujerar majalisar wakilai ya koma PDP

Hadiza Gabon ta bawa Rabiu Arrahus tallafin N500,000

Hadiza Gabon ta bawa Rabiu Arrahus tallafin N500,000
Source: Facebook

Sha'aban ya bayyana hakan ne a shafinsa na Instagram mai suna tyshaban inda ya bukaci sauran abokan aikinsu na Kannywood su taimaka ta kowane halli da suke da shi.

Jarumin daga bisani ya sake wallafa wani sakon a shafin sada zumuntar inda ya ke yabawa Gabon bisa gudunmawar da ta bayar yayin da mai bayar da umurni a fina-finai, Hassan Giggs shima ya yi amfani da shafinsa na instagram, hassan_giggs ya yabi jarumar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa Sarkin Kannywood, Ali Nuhu shima ya baiwa mara lafiyar tallafi sai dai ba a bayyana adadin kudin da Ali ya bayar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel