Hotunan sabuwar sansanin horas da Sojin Saman da aka kaddamar a Bauchi

Hotunan sabuwar sansanin horas da Sojin Saman da aka kaddamar a Bauchi

A yau, Juma'a 31 ga watan Janairu ne Shugaban Hafsin Sojojin Sama na Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar ya kaddamar da sansanin horas da dakarun sojin saman Najeriya na musamman a garin Bauchi.

An kafa wannan sansanin ne domin cigaba da bayar da horo ga sojojin Najeriya a yakin da su keyi da 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas na kasar nan.

Bugu da kari, sansanin zai kasance wurin karo ilimi da samun kwarewa a fanoni daban-daban na aikin sojan domin inganta ayyukansu.

Taron ya samu hallartar manyan dakarun sojojin saman Najeriya da ma wasu bakin.

Ga hotunan yadda taron kaddamarwar ta kasance a kasa:

Hotunan sabuwar sansanin horas da Sojin Saman da aka kaddamar a Bauchi

Shugaban Hafsin Sojojin Sama na Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar yayin da ya ke isowa wurin taron kaddamar da sansanin soji a Bauchi
Source: Facebook

Hotunan sabuwar sansanin horas da Sojin Saman da aka kaddamar a Bauchi

Shugaban NAF, Air Marshal Sadique Abubakar yana bayar da jawabin bude taro a Bauchi
Source: Facebook

Hotunan sabuwar sansanin horas da Sojin Saman da aka kaddamar a Bauchi

Dakarun Sojojin Saman Najeriya yayin da suke karbar umurni daga jagorarsu a wurin kaddamar da sansanin sojin na Bauchi.
Source: Facebook

Hotunan sabuwar sansanin horas da Sojin Saman da aka kaddamar a Bauchi

Dakarun NAF suna paretin ban girma ga Shugaban Hafsin Sojojin Sama na Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar
Source: Facebook

Hotunan sabuwar sansanin horas da Sojin Saman da aka kaddamar a Bauchi

Shugaban Hafsin Sojojin Sama na Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar yana kaddamar da wani gini a sansanin sojin na Bauchi
Source: Facebook

Hotunan sabuwar sansanin horas da Sojin Saman da aka kaddamar a Bauchi

Dakarun sojin saman yayin da suke atisayen kai farmaki ga 'yan ta'adda da ceto wadanda ake garkuwa da su
Source: Facebook

Hotunan sabuwar sansanin horas da Sojin Saman da aka kaddamar a Bauchi

Dakarun Soji yayin da suke samun horo na dabarun yaki da 'yan ta'adda a filin daga
Source: Facebook

Hotunan sabuwar sansanin horas da Sojin Saman da aka kaddamar a Bauchi

Wasu daga cikin dakarun Sojin Saman Najeriya da suka hallarci kaddamar da sansanin sojin a jihar Bauchi
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Dakatar da Onnoghen: Matasa sun yiwa shugaban kungiyar lauyoyi duka a jihar Ribas

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel